Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta tabbatar wa da sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa cewa abubuwa sun sauya a Nijeriya.

Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro a Nijeriya Mallam Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin Bola Tinubu za ta tabbatar wa da sabuwar ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa da ke arewa maso yammacin ƙasar cewa abubuwa sun sauya, ta hanyar fatattakarta daga Nijeriya.

Mallam Ribadu ya yi wannan magana ce a lokacin da yake wakiltar Shugaba Tinubu a wajen bude wani Babban Taro na Shugabannin Hukumar Kwastam na 2024, a ranar Laraba a Abuja.

A makon da ya wuce ne Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta bayyana ɓullar sabuwar ƙungiyar ta’addancin ta Lakurawa a jihohin Sokoto da Kebbi, inda ta ce sun shiga ƙasar ne daga Jamhuriyar Nijar da Mali.

Sai dai masana harkokin tsaro sun ce dama ƙungiyar Lakurawa ta daɗe a Nijeriya tun shekarar 2018. “Za mu fatattaki wadanda ake kira Lukarawa daga ƙasarmu.

Za mu kunyata masu suka kuma mu rufe bakunansu ba tare da ɓata lokaci ba. Boko Haram da suka addabi kasarmu, yanzu sun fara gudu. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu ƙasashe maƙwabta saboda a yanzu ba sa jin daɗin Nijeriya wajen gudanar da ayyukansu,” in ji shi.

''An samu ci gaba a mulkin Tinubu"

Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaron, NSA ya ce ba tare da saka siyasa kamar yadda aka saba ba a ko yaushe, an cim ma nasarori a ɓangarori da dama a Nijeriya tun bayan hawan Shugaba Tinubu mulki a watan Mayun 2023.

Ya kuma ce alamun da ke nuna cewa al’amura na ƙara inganta ta fuskar tattalin arziki a bayyane suke kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da ƙaruwar haƙko ɗanyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi a matsayin wani bangare na irin wannan kokarin.

“Haƙar ɗanyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 sannan kuma an tsaftace Babban Bankin Ƙasa; babu wanda ke karɓar ko kobo daga CBN. A lokacin da muka yi alkawarin cewa za mu gyara kasar nan, za mu yi hakan ne domin Shugaba Tinubu bai taɓa gazawa ba,” in ji Mallam Ribadu.

A cikin jawabin da NSA ɗin ya gabatar a madadin Tinubu, ya ce Shugaban Ƙasar ya tashi tsaye da hangen nesa mai tushe don ƙarfafa tushen tattalin arzikin Nijeriya da samar da ci gaba mai kyau don amfanin kowa, yana mai alkawarin cewa bayan watanni 18, burikan ba su sauya ba.

A ƙarshe a saƙon Shugaban Ƙasar, Mallam Ribadu ya yaba wa hukumar Kwastam bisa yadda ta sa hannu a cikin manufofinsa ta hanyar ƙarfafa matsayin Nijeriya a matsayin kasa mai hulda da kasuwanci ta hanyar yin gyare-gyaren dabaru, musamman a fannin inganta fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da ingancin tashar jiragen ruwa.

Ya kuma jaddada cewa, hidimar ta taimaka matuƙa gaya wajen ganin Nijeriya ta samu ci gaba a duniya da saukin harkokin kasuwanci. .

TRT Afrika