Tiani  bai yi cikakken bayani kan lokaci da kuma tsarin samar da kudin ba, ko da yake ya ce matakin na daya daga cikin dalilan da suka sa ya kai ziyara kasashen biyu kwanakin baya./Hoto:Fadar Shugaban Nijar

Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ya ce kasarsa da Mali da kuma Burkina Faso za su samar da kudin bai-daya domin karfafa tattalin arziki da ci-gabansu.

Janar Abdourahamane Tiani a gidan talbijin na RTS ranar Lahadi da maraice.

Sai dai bai yi cikakken bayani kan lokaci da kuma tsarin samar da kudin ba, ko da yake ya ce matakin na daya daga cikin dalilan da suka sa ya kai ziyara kasashen biyu kwanakin baya.

"Baya ga karfafa harkokin tsaro, dole kawancenmu ya samu tagomashi ta fuskar siyasa da sha’anin kudi," in ji shi.

A halin yanzu dai kasashe takwas a Yammacin Afirka, ciki har da Nijar da Mali da Burkina Faso, suna yin amfani da CFA, kudin da Faransa ta kakaba musu tun zamanin mulkin-mallaka abin da mazauna yankin suke matukar adawa da shi.

Labari mai alaka: Sahel Alliance: Nijar, Burkina Faso da Mali sun kulla kawance

Dama dai tuni kasashen uku suka kafa kungiyar kawance ta Alliance of Sahel States (AES) da zummar tunkarar matsalolin tsaron da ke addabarsu da kuma far wa duk wata kasa da ta taba daya daga cikinsu.

Haka kuma a farkon watan nan ministocin kasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar sun bayar da shawarar kirkiro tarayyar kasashen uku a wani bangare na hada kan kasahen don su zama a dunkule wuri daya.

Kasashen uku, wadanda suke karkashin mulkin soji, sun zare kansu daga cikin kungiyar kasashen G5 Sahel wadda ke hada gwiwa da Faransa domin tabbatar da tsaro a yankin Sahel.

Kazalika sun gargadi kungiyar ECOWAS da ta guji yunkurin amfani da karfin soji a kan Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Julin da ya gabata.

TRT Afrika da abokan hulda