Sojojin sun ce suna gudanar da bincike kan gungun. Hoto/Nigeria Army

Bataliya ta 192 ta rundunar sojin Nijeriya ta kama wani gungu na kasa da kasa da ke fasa-kwaurin muggan makamai.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, an kama gungun ne a hanyar Anambra a ranar Asabar a lokacin da yake safarar harsasai masu dumbin yawa da ke cikin wata babbar mota.

“Dakarun wadanda suka yi aiki bisa bayanan sirrin da suka samu, sun gudanar da binciken kan motoci a kan hanyar Ajilete zuwa Owode da ke Yewa North a Jihar Ogun.

“Sun gano makamai a cikin wata babbar mota mai lamba ENU 697 XY cike da fakiti 720 na jajjayen harsasai wanda a ciki ake samun harsasai 25 a ciki,” in ji sanarwar. Sojojin sun ce jimlar harsasan da aka samu sun kai 18,000.

Jimlar harsasai 18,000 ne aka samu a cikin motar. Hoto/Nigeria Army

Wadanda ake zargin sun hada da Mista Seworvor wanda dan kasar Ghana ne da direban motar mai suna Mista Lukman Sani, tuni aka kama su inda kuma ake gudanar da bincike, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma sojojin sun ce binciken wucin gadin da suka yi ya nuna cewa makaman wadanda aka yi fasa-kwaurinsu, an dauko su ne tun daga kasar Mali inda aka boye su cikin wata mota wadda aka shigo da ita daga can ta iyakar Idiroko.

Rundunar sojin Nijeriya dai ta sha jaddada cewa tana ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da tsaro a Nijeriya.

Ko a makon da ya gabata sai da sojojin suka ragargaji ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.

TRT Afrika