Namibia ta soki matakin da Jamus ta dauka na goyon bayan "Isra'ila game da kisan kare-dangin da take yi wa fararen-hula da ba su da laifi a Gaza."
Shugaban Namibia Hage Geingob ya ce sukar da Jamus ta yi wa Afirka ta Kudu saboda gurfanar da Isra'ila a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a kan kisan kare-dangin da take yi a Gaza ya "girgiza" kasarsa.
Matakin da Afirka ta Kudu ta dauka na kai Isra'ila kara a kotun ICJ ya ja hankalin duniya inda ake ta yabonta kuma ake kallonsa a matsayin wani gagarumin "tarihi".
Sai dai wasu kasashen yammacin duniya ciki har da Jamus sun soki matakin. Kazalika Isra'ila ta musanta cewa tana aikata kisan kare-dangi a Gaza.
'Matakin da bai dace ba'
Jamus ba ta da kimar da za ta kare "gwamnatin Isra'ila bisa kisan kare-dangi da take yi wa fararen-hula da ba su da laifi a Gaza da yankin Falasdinu da aka mamaye," in ji Namibia.
''A kasar Namibia, Jamus ta gudanar da kisan kare-dangi na farko a karni na 20 daga shekarar 1904-1908, inda dubban 'yan kasar Namibia da ba su ji ba, ba su gani ba suka mutu cikin wulakanci," kamar yadda Fadar shugaban kasar Namibia ta bayyana a wata sanarwa ranar Asabar da maraice.
Shugaba Geingob ya yi kira ga Jamus ta "sake nazari kan wannan mataki da ta dauka da bai dace ba inda ta kasance mai goyon bayan kisan kare-dangi da Isra'ila take yi".
Isra'ila ta kashe Falasdinawa fiye da 23, 000 tun ranar 7 ga watan Oktoba da ta kaddamar da hare-hare a Gaza. Kazalika sama da kashi 85 na al'ummar yankin su miliyan 2.3 sun rabu da matsugunansu.