Mutanen da suka mutu a birnin Derna na kasar Libya sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta fada wa kasar za si iya kai wa tsakanin 18,000 zuwa 20,000, a cewar Magajin birnin a hira da gidan talbijin na Al Arabiya.
Abdulmenam al Ghaithi ya yi hirar ce ranar Laraba da maraice inda ya kiyasta cewa sun tattara alkaluman ne daga yankunan da bala’in ya auku.
Dubban mutane ne suka bata yayin da wasu dubban suka tagayyara, a cewar hukumomin kasar da na bayar da agajin gaggawa.
Ambaliyar ruwa wadda mahaukaciyar guguwa da aka yi wa lakabi da 'Daniel' da ta girgiza kasar ranar Lahadi ta fi shafar birnin Derna da ke gabar tekun Bahar Rum bayan da ta fasa wasu madatsun ruwa biyu inda ruwa ya rika tuttuda a yanayi irin na tsunami.
Kasashen duniya irin su Turkiyya da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa na cikin sahun farko wajen kai wa kasar agaji.
Labari mai alaka: Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 6,000 a Libya
Kakakin ma’aikatar cikin gida ta Libya Laftanar Tarek al-Kharraz ranar Laraba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum 3,840 aka bayar da rahoton mutuwarsu a birnin, cikinsu har da mutum 3,190 da tuni aka binne su.
Ya kara da cewa wadanda aka binne har da mutum 400 ‘yan kasashen waje, galibinsu ‘yan kasar Sudan da Masar.
Ranar Laraba karamin sakataren Ma'aikatar Lafiya na gwamnatin Libya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya cewa wadanda suka mutu sun wuce 6,000, kuma dubbai sun bata.