Ana yawan samun ambaliyar ruwa a Nijar a duk shekara. Hoto/UNICEF

Hukumomi sun ce akalla mutum 32 ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa a Jamhuriyar Nijar.

An samu ambaliyar ne bayan ruwan saman da aka zabga kamar da bakin-kwarya a ‘yan makonnin baya, a cewar sanrwar da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta bayar ranar Juma'a.

Yankin Tahoua da ke kudancin kasar ne matsalar ta fi kamari inda mutum 12 suka rasu sai kuma mutum 10 suka rasu a Maradi.

A Zinder kuwa mutum shida suka rasu sai Tillaberi mutum biyu suka rasa rayukansu da Niamey da Diffa mutum daya kowanensu.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum tara cikin wadanda suka rasu gidajensu ne suka rufta sakamakon ambaliyar sai kuma mutum 23 da suka rasu nutsewa suka yi, kamar yadda ma'aikatar cikin gida ta Nijar ta tabbatar.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa ruwan saman da ake yi a Nijar a kowace damina na haddasa asarar rayuka da dama.

Ko a bara sama da mutum 100 ambaliyar ta kashe a Jamhuriyyar Nijar haka kuma ambaliyar ta kashe dabbobi da dama da kuma lalata gonaki.

Ambaliyar ruwan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan kasar ke fama da matsin rayuwa sakamakon takunkuman da aka saka wa kasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

TRT Afrika