Nijeriya da China za su samar da na'urar gano yiwuwar girgizar kasa

Nijeriya da China za su samar da na'urar gano yiwuwar girgizar kasa

Babu cikakken bayani game da shirin amma a yanzu haka jami'an China suna wata ziyara a Abuja.
Na'urar za ta tattaro bayanai ne daga doron kasa ko sararin samaniya. Hoto: NTA

Nijeriya da China za su hada gwiwa domin samar da wata na'ura karon farko da za ta sanya ido kan yiwuwar faruwar girgizar kasar.

Gidan talbijin na kasa a Nijeriya, NTA, ya rawaito cewa za a samar da nau'arar ce domin gano yiwuwar aukuwar girgizar kasa a Nijeriya da kuma sauran kasashen Afirka na kudu da Sahara.

Babu cikakken bayani game da shirin amma a yanzu haka jami'an China suna wata ziyara a Abuja.

Na'urar za ta tattaro bayanai ne daga doron kasa ko sararin samaniya.

Daga nan za ta sarrafa su ta tantance taririnsu game da yiwuwar faruwar girgizar kasa yadda kasashen za su kasance cikin shiri.

Wani rahoton hadin gwiwa da UNESCO da Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Afirka da Hukumar Taswirar Kasa ta Duniya suka fitar a 2015 ya bayyana wanzuwar gocacciyar kasa a Afirka na saka barazanar yiwuwar samun girgizar kasa babba ko motsawarta.

Ana kallon yankin Yammacin Afirka da ya faro daga Nijeriya zuwa Senagal a matsayin mafi karancin hatsarin fuskantar girgizar kasa, kamar yadda binciken ya bayyana.

TRT Afrika