Cecilia Abena Dapaah ta ce ta ajiye aikinta ne don kada batun shari'ar da take yi ya karkatar da hankulan jama'a daga ayyukan gwamnatin Ghana./Hoto: Ghana News Agency

Ministar Albarkatun Ruwa da Tsaftace Muhalli ta Ghana Cecilia Abena Dapaah ta ajiye aikinta.

Ta bayyana haka ne a wata takarda da ta sanya wa hannu a yau Asabar 22 ga watan Yulin 2023.

Dapaah ta sauka daga mukaminta ne jim kadan bayan ta ce za ta yi karin bayani game da wasu rahotanni da ke cewa an sace fiye da $1.3 m daga gidanta da ke Accra babban birnin kasar.

Wasu bayanai sun yi zargin cewa masu yi wa Dapaah aikace-aikace a gida ne suka sace kudaden tsakanin watan Yuli zuwa Oktoba na 2022.

Kamfanin dillancin labarai na Ghana News Agency ya rawaito cewa kudin na kasashen waje ne da kuma na cikin gida.

Rahotanni sun ce an sace $1 m, €300,000 da kuma miliyoyin kudin Ghana wato cedi, inda jimillarsu ta kai $1.3 m daga gidan Dapaah.

Wannan batu ya jawo muhawara mai zafi a cikin kasar.

Dauke hankalin gwamnati

A cewar Dapaah, kafafen watsa labarai "sun cika da labarai game da shari'ar da ake yi a kan satar da aka yi a shekarar da ta wuce a gidan da nake zaune tare da mijina da 'yata.

Labaran sun ce ni na mallaki makudan kudade na kasashen waje da kudin Ghana cedi wadanda aka sace daga gidana.

Ina so na bayyana karara cewa wadannan kudi ba su ne adadin da na kai kara a kansu a wurin 'yan sanda ba, amma duk da haka ina sane da tasirin wannan labari a kan mutum mai rike da mukami irin nawa."

Ministar ta kara da cewa don haka ne ta ga ya kamata ta ajiye mukaminta "saboda ba na so wannan batu ya zama abin da zai dauke hankalin gwamnati ya hana ta gudanar da ayyuka a irin wannan lokaci mai muhimmanci."

An ajiye kudin a gida

Ana zargin cewa ministar da mijinta Daniel Osei Kuffour, sun ajiye kudin ne a gidansu da ke unguwar attajirai ta Abelempke da ke arewacin Accra.

Rahotannin sun ce a kwanakin baya ne Dapaah ta kai karar masu yi mata aikace-aikace a gida, Patience Botwe da Sarah Agyei, a kotu bisa zargin sace mata kudin tsakanin Yuli zuwa Oktoba na bara.

Ranar Alhamis aka gurfanar da Botwe da Agyei da karin mutum uku da ake zargi, cikinsu har da wani mai gyaran famfo a kotun Accra.

Kazalika ana zargin masu yi mata aikace-aikacen da sace tufafi da sarkoki da turare da kuma jakunkunan hannu na Dapaah wadanda suka kai dubban dalar Amurka.

Rahotanni sun ce a watan Yunin wannan shekarar ne Dapaah ta fahimci cewa an sace kudin da sauran kayan nata, abin da ya sa ta mika batun ga rundunar 'yan sanda har aka kama mutanen da ake zargi.

An sayi gida da kudin

Masu yi wa Cecilia Abena Dapaah aikace-aikace sun shaida wa alkaliyar kotun Accra Susana Ekuful cewa sun yi amfani da kudin wurin sayen motoci da gida mai daki uku a birnin Tamale da ke arewacin Ghana.

An saki daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Agyei, bayan an biya kudi belin da suka kai cedi miliyan daya saboda ba ta dade da haihuwa ba. Ana ci gaba da tsare sauran mutum hudu kafin ranar 2 a watan Agusta inda za a ci gaba da sauraron kara.

'Yan sanda sun ce kawo yanzu an kwato akalla $46,260 daga wurin mutane.

TRT Afrika