Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a ranar Laraba ya halarci wani taron ƙungiyar hadin gwiwa na ƙasarsa da Jamhuriyar Nijar a birnin Niamey. Ya kai ziyara ne Nijar ɗin ne ta tsawon wuni ɗaya.
Fidan ya kai ziyarar ƙarƙashin rakiyar Ministan Tsaron Turkiyya Yasar Guler da Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa Alparslan Bayraktar da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri Ibrahim Kalin da Sakataren Masana'antun Tsaro Haluk Gorgun da kuma Mataimakin Ministan Kasuwanci Ozgur Volkan.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar a shafinta na X cewa Firaministan Nijar li Mahamane Lamine Zeine ne ya jagoranci taron.
Majiyoyin diflomasiyya a ranar Talata sun ce ana sa ran taron na ƙasashen biyu zai mayar da hankali ne kan dangantakar tattalin arziki da siyasa da kuma abubuwan da ke faruwa a yanzu haka a yankin Sahel, da ma batutuwan da suka shafi yanki, ciki har da rikicin Isra'ila da Falasɗinu.