Wani rahoton bincike da sauraron al'umma kan cin zarafin mata a Ghana ya nuna cewa matan da aka yi lalata da su ba su cika fitowa fili suna neman taimako ba saboda gudun nuna musu kyama.
Cibiyar bunkasa kiwon lafiya da bincike a Ghana (CEHDAR) tare da tallafin Asusun Raya ci-gaban Mata na Afirka (AWDF) da kuma kungiyar White Ribbon Alliance na kasar Kenya ne suka gudanar da binciken karkashin wani shiri na shekara uku mai suna KASA, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Ghana GNA ya bayyana.
“Yawancin matan da ake cin zarafin su ta hanyar lalata ba sa iya fitowa fili su yi magana saboda matsalar rashin kudi da kuma hanyar da za su bi wajen samun taimako,” a cewar rahoton.
KASA, wani shiri ne da ya mayar da hankali kan yadda laifuffukan lalata da ake yi wa mata da kuma cin zarafi tsakanin jinsi ke dada karuwa, da kuma samar da hanyoyin habaka ayyukan mata da ba da shawarwari don rage cin zarafin da ake yi wa matan a kasashen Ghana da Nijeriya da kuma Senegal.
A hirar da GNA ya yi da Dokta Jemima Dennis-Antwi, shugabar Cibiyar CHEDAR, ta ce binciken da suka yi ya biyo bayan bukatar samar da hanyoyin da za a iya dakile ayyukan cin zarafi da kuma yadda mata da ‘yan mata za su iya kare kansu daga cin zarafi, da kuma yadda su kansu wadanda abin ya shafa za su taimaki kansu sannan al’umma ita ma ta taimaka musu.
“Rahoton ya yi nuni da cewa al'ada da yanayin zamantakewa da gazawar doka da kuma rashin kudi ne makasudin abubuwan da ke hana matan iya magana balle su kai rahoton abin da ya faru da su,’’ in ji Dakta Jemima, tana mai cewa akwai bukatar a samar da cikakken tsarin da zai tallafawa matan ta kowacce fuska.
"Ayyukan cin zarafi yana haifar da mummunan sakamako ga lafiyar jiki da kwakwalwar matan da aka yi wa, sannan yana da tasiri ga tsarin kiwon lafiya da shari'a da kuma walwalar al’umma baki daya," in ji Daktar.
Rahoton ya bukaci a inganta ayyukan ba da shawarwari da kuma kebe wani wuri na musamman da za a tsugunar da wadanda suka fada cikin irin wannan yanayi, sannan hukumomi su samar da matakan gaggawa da kuma tilasta bin doka.
Kazalika rahoton ya jaddada bukatar kara wayar da kan jama'a game da cin zarafi ta hanyar lalata da samar da hanyoyin ba da ilimi a makarantu game da jima'i da kuma hulda da kafafen yada labarai don kara yada manufar.
Rahoton ya bukaci a samar da wani shiri da zai taimaka wa matan da lamarin ya shafa da kuma karfafa musu gwiwar fitowa su yi magana kan abin da ya faru da su.
GNA ya bayyana cewa binciken "Shugabannin al'umma da cibiyoyin addini da kungiyoyin jama'a suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen ci gaba da wayar da kan jama'a da kuma taimaka wa wajen dakile matsalar ta cin zarafi" a cewar rahoton.