Gaba ɗaya, an sauya sunayen tituna kusan 25, daga cikinsu akwai ƙanana da lunguna da manyan tituna har ma da wasu wuraren taron jama'a. / Hoto: AFP

Mali ta bi sahun Burkina Faso da Nijar a ranar Larabar da ta gabata wajen sauya sunayen tituna da manyan tituna a babban birnin kasar don kawar da sunayen Faransawa 'yan mulkin mallaka.

An sake sauya titunan da ke dauke da sunayen 'yan mulkin mallaka na Faransa a Bamako, a cewar wata doka da hafsan sojin kasar ya bayar.

Titin Cedeao Avenue (wanda da Faransanci yake nufin Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ko ECOWAS) a yanzu an mayar da shi sunan sabuwar ƙungiyar hadin kai wadda Mali da Burkina Faso da Nijar suka kafa - wato Ƙungiyar Kasashen Sahel (AES).

Gaba ɗaya, an sauya sunayen tituna kusan 25, daga cikinsu akwai ƙanana da lunguna da manyan tituna har ma da wasu wuraren taron jama'a.

Nijar ta sauya sunayen wurare masu tarihi

Da ma Nijar da Burkina Faso sun riga sun yi sauye-sauye da dama kan sunayen tituna da abubuwan tarihi a cikin shekaru biyu da suka wuce.

A watan Oktoba, Nijar ta sauya sunan wasu wurare masu tarihi a Yamai babban birnin kasar wadanda a baya suna da alaka da tsohuwar kasar da ta yi musu mulkin mallaka, Faransa.

Sojoji ne ke mulkin kasar Mali tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekara ta 2020 da 2021.

Karkashin mulkin Kanar Assimi Goita, Mali ta karya yarjejeniyar da aka dade tana yi da kawayenta na Turai da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, a maimakon haka ta koma ga Rasha da kungiyar mayaƙan haya ta Wagner domin samun tallafi.

AFP