Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce kasafin kudin da ya gabatar wa Majalisar Dokokokin kasar na Naira tiriliyan 47.9 na daya daga cikin hanyoyin farfado da Nijeriyar.
Tinubu ya gabatar da kasafin kudin wanda ya zama karo na biyu tun bayan hawansa, a ranar Laraba a gaban ‘yan majalisar wakilai da na dattijai.
Ya je majalisar ne ƙarƙashin rakiyar Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila da sauran manyan jami’an gwamnati.
Kasafin kudin 2025 da na gabatar a yau a zaman hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa na ɗaya daga cikin hanyoyin farfaɗo da Nijeriya.
“Zai hada kan muhimman manufofin da muka bullo da su domin sake fasalin tattalin arzikinmu da bunkasa manyan ayyukan raya ƙasa da ƙara yawan ciniki da zuba jari da ƙarfafa samar da man fetur da iskar gas da sake farfado da masana'antunmu da kuma ƙara karfin tattalin arzikinmu,” a cewar saƙon da shugaban ya wallafa a shafinsa na X bayan gabatar da kasafin.
Ya jaddada cewa tafiyar sabunta tattalin arziki da ci gaban hukumomi, wanda muka fara watanni 18 da suka gabata a matsayin al'umma, tana aiki sosai.
“Ba tafiya ce don zaɓinmu ba, muna yin ta ne don mu ciyar da Nijeriya gaba. Ina gode wa dukkan ‘yan Nijeriya da muke wannan tafiya ta sauye-sauye da ci gaba a tare,” ya ce.
A cewar Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Atiku Bagudu, ana hasashen kudaden da za a kashe a shekarar 2025 za su kai Naira tiriliyan arba’in da bakwai da biliyan dari tara da sittin, wanda hakan ya ƙaru da kashi 36.8 bisa 100 a kan na shekarar 2024.
Bagudu ya ce an kasafin kudin shekarar 2025 a kan farashin man fetur da ya kai dala 75 kan kowacce gangar mai, inda za a dinga hakar mai na ganga miliyan 2.06 a kowace rana, a kan canjin Naira 1,400 kan duk dala daya.
Sauran bayanan Shugaban Kasar
Kazalika, Shugaban Ƙasar ya ce ƙudurin kasadin na 2025 yana sake karfafa taswirar gwamnatinsa don tabbatar da zaman lafiya da wadata da fatan samun makoma mai kyau ga ƙasar.
Tinubu ya kuma bayyana nasarar da ya ce gwamnatinsa ta samu wajen aiwatar da kasafin kudin 2024 kamar haka: - Naira tiriliyan 14.55 na samun kudaden shiga, wanda ya cika kashi 75 cikin 100 na abin da muka sa a gaba a rubu’i uku na shakera.
"An kashe naira tiriliyan 21.60 daga cikin kasafin, wanda ya nuna kashi 85 cikin 100 na abin da muka sa a gaba, shi ma a rubu’i uku na shekarar.
"Yayin da har yanzu ake da kalubale, mun inganta hanyar tattara kudaden shiga kuma mun cika muhimman sharadai.
"A hankali ana jin tasirin wannan sauyi a tattalin arzikinmu. An yi hasashen karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar 2024 mai zuwa da kaso 3.2 cikin dari, kuma sabanin has ashen, kasarmu ta samu ci gaba sosai.
"Tattalin arzikin Nijeriya ya karu da kashi 3.46 a kashi na uku na shekarar 2024, daga kashi 2.54 a rubu’i na uku na shekarar 2023.
"Asusun Ajiyarmu na Kasashen Waje a yanzu ya kai kusan dalar Amurka biliyan 42, yana samar da ingantacciyar kariya daga matsalolin waje.
"Haɓakar fitar da kayayyakinmu zuwa ketare ya bayyana a cikin rarar kasuwancin da ake samu a halin yanzu, wanda a yanzu ya kai Naira tiriliyan 5.8, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana.
"Waɗannan bayyanannun sakamakon da ke nuna ana murmurewa a hankali, da sauransu, suna nuna ƙarfin tattalin arzikinmu da tasirin zaɓin manufofin da muka yi tun farko.
“Sannan ba za mu bar batun wadautwar da abinci a baya ba.”