Gwamnan jihar Oyo na kudu maso yammacin Nijeriya, Seyi Makinde, ya ce an kama mutanen da suka shirya wani taro a wata makaranta inda aka yi turmutsutsun da ya haddasa mutuwar yara da dama a birnin Badun (Ibadan).
Rahotanni dai sun ce an shirya bikin bai wa yara 5000 kyautar naira dubu biyar-biyar ne a filin wasan makarantar boko ta Islamic High School a unguwar Bashorun da ke Ibadan.
Sai dai kuma bikin da tsohuwar matar Ooni na Ile Ife, Sarauniya Silekunola Ogunwusi, ta shirya da haɗakar wani gidan rediyo a birnin na Ibadan ya fuskanci kwararar mutane fiye da yadda aka yi tsammani, lamarin da ya janyo turmutsutsu.
Turmutsutsun ya kashe gomman yara, in ji rahotanni yayin da gwamnatin jihar ta ce an kai wasu da suka ji rauni daga turmutsutsun asibitoci domin kulawa da su.
Da ya kai ziyara ɗaya daga cikin asibitocin da aka kai waɗanda suka ji ciwo a turmutsutsun domin ganin halin da suke ciki, mataimakin gwamnan jihar ta Oyo, Adebayo Lawal, ya ce ba a sanar da gwamnatin jihar ko jami’an tsaro game da taron ba.
“Dole wannan sauraniyar ta miƙa kanta ga ‘yan sanda ba tare da jinkiri ba. Dole kuma mai wannan gidan rediyon ya miƙa kansa,” kamar yadda mataimakin gwamnan jihar ya shaida wa maneman labarai bayan ziyararsa.
A sanawar da ya fitar kan shafinsa na X, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce tuni aka fara bincike kan abin da ya janyo turmutsutsun, yane cewa waɗanda suka shirya taron suna hannu.
“Ina son na tabbatar wa mutanenmu cewa duk wani wanda yake da hannu cikin wannan bala’in za a hukunta shi,” a cewar gwamnan a saƙon da ya wallafa a X.
Ya buƙaci mutane su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro ke bincike game da iftila’in.