Akalla ma'aikatan jinya 4,000 ne daga cikin 10,209 suka samu damar fita daga Ghana don samun rayuwa mai inganci a kasashen ketare./Hoto: GNA

A kalla ma'aikatan jinya 10,209 ne suka nemi izini daga kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Ghana (GRNMA) da nufin barin kasar don samun rayuwa mai inganci, a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Ghana GNA ya fitar.

Ma'aikatan jinyar sun bar kasar ne daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 7 ga watan Yulin 2023.

Daga cikin jumillar ma'aikatan, kusan mutum 4,000 ne kungiyar GRNMA ta share wa fagen fita zuwa wata kasa don samun aiki yi a matsayin ma’aikatan jinya, a cewar Babban Sakataren kungiyar Dakta David Tenkorang- Twum a wata hira da GNA ya yi da shi.

Ya bayyana yadda ficewar ma’aikatan jinya daga kasar ke shafar tsarin kiwon lafiyar Ghana, domin a cewarsa mafi yawa daga cikinsu wadanda suka kware ne sosai a fannin, kuma wadanda ya kamata su horar da na kasa da su.

Dakta Twum ya yi kari da cewa lamarin ya janyo karancin ma’aikatan lafiya a Ghana, inda ya ce a halin da ake ciki sauran ma’aikatan da suka rage na fuskantar matsin lamba.

"Kulawar ma’aikatan jinya abu ne da ake bukata a ko da yaushe, idan wadanda ya kamata su taimaka suka bar kasar, hakan na nufin wadanda suke kasa dole su kara lokacinsu na aiki kuma yin hakan ba karamin kalubale zai haifar ba ga tsarin yanayin aikin." in ji shi.

Wanda ya yi aiki na tsawon shekaru yana da kwarewa da gogewar da dole mu mayar da hankali kar a rasa shi, a cewar likitan.

"Za a samu gibi sosai tsakanin sabbin ma’aikatan da ke aiki yanzu da wadanda suka shafe kusan shekara 10 suna aiki kuma yanzu sun bar kasar."

Kwararru sun danganta yawan barin kasar da ma'aikatan jinya na kasashen Afrika ke yi zuwa ketare da yanayin rashin inganta tsarin aiki da rashin biyansu isasshen kudaden albashi da alawus-alawus da kuma tabarbarewar yanayin tattalin arzikin na kasashensu.

Masana na ganin idan ba a gagguta magance lamarin ba za a ci gaba da rasa kwararrun ma’aikatan lafiya.

TRT Afrika