Wasu kasashen kungiyar hadin kan Larabawa sun goyi bayan ikon kasar Somaliya a kan yankunanta. / Hoto: AA  

Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta sanar da cewa za ta kira wani taron gaggawa na ministocin kasashen da take wakilta kai tsaye ta intanet domin tattauna batun takun sakar da ke tsakanin Somaliya da Habasha.

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hossam Zaki ya ce kungiyar kasashen Larabawan za ta gudanar da taron ne a ranar Laraba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA ya ruwaito.

Zaki ya ce taron zai mayar da hankali ne kan sakamakon yarjejeniyar da aka rabbata wa hannu ''ba bisa ka'ida ba" tsakanin Habasha da yankin Somaliland da ya balle daga kasar Somaliya wanda ke baiwa Addis Ababa ayyuka a yankin arewa maso yammacin Somaliya na tekun Bahar Maliya.

Ya bayyana cewa Moroko ce za ta jagoranci taron, tare da kari kan cewa shawarar hakan ya biyo bayan bukatar Somaliya da kuma goyon bayan kasashen Larabawa 12.

Kazalika ya bayyana samun cikakken goyon bayan da ake da shi ga matsayar Somaliya.

Gargadi

Firaministan Somaliya Hamza Abdi Barre ya fada a ranar Asabar cewa yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) ba ta da ''wani inganci'', ya yi gargadi Habasha kan duk wani katsalandan ko kutse kai kan yankunan Somaliya.

Sakamakon yarjejeniyar ruwa da Habasha ta kulla da Somaliland a farkon watan Janairu, gwamnatin Somaliya ta yi wa jakadanta da ke Habasha kiranye.

Kungiyar kasashen Larabawa da dama, ciki har da Masar sun bayyana sun yi fatali da yarjejeniyar tare da bayyana goyon bayansu ga ikon Somaliya a kan yankunanta.

Somaliland, wacce ta ayyana samun 'yancin kai daga Somaliya a shekarar 1991, ta baiwa Habasha damar amfani da gabar tekunta domin kasuwanci da kuma harkokin soji, ta hanyar yerjejeniyar 'MoU' da aka rattabawa hannu a ranar 1 ga watan Janairu, ciki har da tashar jiragen ruwa ta Berbera mai matukar mahimmanci.

Zanga-zanga

Somaliland ta sanar da cewa Habasha za ta amince da ita a matsayin kasa mai cin gashin kanta bayan kammala yarjejeniyar.

A martanin da aka mayar kan wannan mataki, daruruwan mutane a Somaliya sun yi zanga-zangar nuna adawa da Habasha, ciki har da wasu fitattun mutane 'yan Somaliya.

Habasha ta yi asarar tashoshin jiragen ruwanta na tekun Bahar Maliya wato Red Sea a shekarun farkon na1990 bayan yakin neman 'yancin kai na Eritriya, wanda ya gudana daga shekarar 1961 zuwa 1991.

A shekarar 1991 ne Eritrea ta sami 'yancin kai daga Habasha, wanda ya kai ga kafa kasashe biyu daban-daban.

Rabuwar da kae ya yi sanadin rasa hanyar shiga tekun bahar Maliya da Habasah ta yi kai tsaye tare da manyan tasoshin jiragen ruwa.

Habasha ta dade tana fama da matsalar rashin hanyar ruwa, lamarin da ke shafar yanayin gudanar da kasuwancinta ruwa yadda take.

TRT Afrika