Birtaniya ta amince ta kulla yarjejeniya da kasar Zambiya kan makamashi mai tsafta da wasu ma'adanai masu muhimmanci.
Hakan na zuwa ne bayan kawo karshen ziyarar kwanaki hudu da ministan harkokin wajen Birtaniya James Cleverly ya kai nahiyar Afirka domin karfafa alakar da ke tsakaninsu.
Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta ce Cleverly zai amince da wata yarjejeniya ta ma'adinai mai suna ''Growth Green'' tsakanin Birtaniya da Zambia, don samun fam biliyan 2.5 (dala biliyan 3.17) daga hannayen jarin kamfanoni masu zaman kansu na Birtaniya da ke bangaren hakar ma'adinai a Zambiya da kuma bangaren sabunta makamashin kasar
A bangaren gwamnati kuwa ita za ta zuba hannun jarin fam miliyan 500.
"Shirin aikin Green Growth na Birtaniya da Zambia da yarjejeniyarmu kan ma'adinai masu muhimmanci za su taimaka wa hanyoyin zuba jari tsakanin Birtaniya da Zambia tare da samar da ayyukan yi a kasashen biyu," a cewar Cleverly.
Arzikin ma'adinai
Zambiya na daya daga cikin kasashen da ke samar da fararen-karafa a duniya sannan tana da manya-manyan ma'adinai kamar cobalt da manganese da nickel.
A bara, Birtaniya ta jaddada mahimmancin sake dabarun samar da wasu hanyoyin samun ma'adinanta.
Cleverly zai kai ziyara wani wurin hakar ma'adinan farin- karafa a Zambiya tare da sanya hannu kan yarjejeniyar kan wasu ma'adinan, wanda Birtaniyya ta ce "zai kafa ci gaban tallafin da Birtaniya za ta samar don hako ma'adinan farin-karfe da cobalt da sauran wasu karafa masu muhimmanci don samar da tsabtataccen sauyi na makamashi ga duniya."
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu masana ke bayyana damuwarsu kan abin da suka kira sabon yanayi na ‘tarwatsa’ albarkatun kasa na Afirka da kuma illar da ke tattare hakan ga ‘yan Afirka.
Ministan na Birtaniya ya yi amfani da ziyararsa wajen karfafa alakar Birtaniya da nahiyar Afirka, inda ta yi wa yankin maraba da tattaunawa kan rikicin Nijar tare da bayyana tallafi kasarsa ga fannin noma a Najeriya.