Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya shaida wa taron koli da shugabannin kasashen Afirka a St. Petersburg cewa Rasha za ta maye gurbin Ukraine wajen fitar da hatsi zuwa kasashen Afirka.
Shugaban ya ce Moscow za ta shirya fara samar da hatsi kyauta ga kasashen Afirka shida cikin wata uku zuwa hudu da ke tafe.
Ya bayyana sunayen kasashen wadanda suka hada da Burkina Faso da Zimbabwe da Mali da Somaliya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Eritrea, inda ya ce kowacce daga cikinsu za ta samu tan 25,000 zuwa 50,000.
A shirye Rasha take ta hada kai da kasashen Afirka wajen bunkasa kudadensu don kara darajar tattalin arzikin yankunansu a cewar shugaban.
Taron kolin Rasha da Afirka shi ne irinsa na biyu da aka taba gudanarwa bayan taron farko da aka yi a shekarar 2019 a birnin Sochi na kudancin kasar Rasha.
Ana sa ran Putin zai jagoranci wata tattaunawa ta musamman da takwarorinsa tare da gabatar da jawabi a zauren zaman taron.
Tattaunawa daga bangarorin biyu
A tsawon shekara daya, yarjejeniyar da aka yi ta ba da dama a fitar da kusan tan miliyan 33 na hatsi daga tashoshin jiragen ruwa na Ukraine, yanayin da ya taimaka wajen daidaita farashin abinci a duniya da kuma kawar da karancin abinci.
Moscow dai ta yi kokari wajen kwantar wa abokan huldarta na Afirka hankula, tana mai cewa ta fahimci "damuwarsu" kan batun, kuma a shirye take ta fitar da hatsi kyauta zuwa kasashen Afirka da ke da bukatarsa.
Putin zai kuma tattauna kan batun Ukraine yayin liyafar cin abincin rana tare da wasu manyan shugabannin kasashen Afirka da aka shirya yi a ranar Juma'a, a cewar Fadar Kremlin.
Tuni dai Putin ya tattauna da Firaministan Habasha Abiy Ahmed da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi a jiya Laraba, inda ya yaba da ayyukan hadin gwiwa da suke yi na shirin samar da makamashi.
Taron na Saint Petersburg na zuwa ne wata guda gabanin taron shugabannin kasashen BRICS (Brazil da Rasha da Indiya da China da kuma Afirka ta Kudu) da zai gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Afirka ta Kudu ta ce Putin, wanda ake tuhumar sa da sammacin kasa da kasa kan rikicin Ukraine, ba zai samu damar halartar taron da kansa ba.