Zambiya ta kwace wani jirgin sama dauke da miliyoyin daloli da gwala-gwalai da makamai

Zambiya ta kwace wani jirgin sama dauke da miliyoyin daloli da gwala-gwalai da makamai

Jami'ai sun ce an kama 'yan kasashen waje takwas don ci gaba da bincike bayan kwace jirgin.
Jirgin ya sauka ne a babban filin jirgin sama na Kenneth Kaunda da ke Lusaka a ranar Litinin da yamma . Hoto:SALIM DAWOOD/ AFP

Hukumomin kasar Zambiya sun sanar da kwace wani jirgin sama dauke da dala miliyan shida lakadan da gwala-gwalai 602 da nauyinsu ya kai kilogiram 127.2 da bindiga biyar da kuma jigidar harsasai 126.

Hukumomin sun kama mutum 10 da suka hada da dan Zambiya daya da 'yan Masar shida da Bajamushe daya da dan Sipaniya daya da kuma dan Latvia, kuma tuni aka tsare su don gudanar da bincike.

Karamin jirgin irin wanda ake daukarsa shata ya shiga kasar ne daga birnin Alkahira na Masar dauke da "kayayyaki masu hadari," sannan ya sauka a babban filin jirgin sama na Kenneth Kaunda da ke Lusaka, babban birnin kasar da misalin karfe bakwai na yammacin kasar ranar Litinin, a cewar shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi a hirarsa da manema labarai.

"Kan wannan bayani ne sai mu da sauran hukumomin tabbatar da doka muka kaddamar da wani aiki da ya kai ga kwace jirgin." a cewar shugaban hukumar, Nason Banda.

Ya ce an kwace jirgin da aka gano kayayyakin a ciki da kuma wani jirgin daban mallakin wani kamfanin jiragen sama na kasar.

Banda ya ce an kai kudaden Babban Bankin Zambiya don ajiyarsu kafin a ci gaba da bincike.

AA