Afirka ta Kudu ba ta bai wa Rasha makamai ba: Bincike

Afirka ta Kudu ba ta bai wa Rasha makamai ba: Bincike

Amurka ta yi zargin cewa Afirka ta Kudu ta kai wa Rasha makamai.
Afirka ta Kudu ta musanta zargin cewa ta mika wa Rasha makamai. Hoto: Reuters

Wani kwamitin bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen cewa Afirka ta Kudu ta bai wa Rasha makamai bai samu wata hujja da ta tabbatar da hakan ba, a cewar fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu a ranar Lahadi.

"Kwamitin ya gano cewa babu wata shaida da aka samu da ta tabbatar da ikirarin cewa wani jirgin ruwa ya yi jigilar makamai daga Afirka ta Kudu zuwa Rasha," in ji wata sanarwa da aka fitar daga ofishin Shugaba Cyril Ramaphosa.

Jakadan Amurka a Afirka ta Kudu, Reuben Brigety, ya shaida wa manema labarai a watan Mayu cewa kasarsa ta gamsu cewa Afirka ta Kudu ta bai wa sojojin Rasha makamai duk kuwa da cewa kasar ta yi ikirarin ba ta da hannu a zargin.

"Daga cikin abin da muka yi la’akari da shi, akwai isowar jirgin ruwan dakon kaya na (Rasha) a sansanin sojin ruwa da ke garin Simon a tsakanin ranar 6 zuwa 8 ga watan Disamba na 2022, wanda muka yi yakinin cewa an dora makamai da alburusai a lokacin da ya dauki hanyarsa ta komawa Rasha," in ji Brigety.

illar zargin

Bayan zargin ne, Ramaphosa ya kafa wani kwamiti mai zaman kansa da wani alkali mai ritaya ya jagoranta domin gudanar da bincike kan batun.

"Kwamitin ya tabbatar da cewa jirgin ruwan mai suna ‘Lady R’ ya tsaya ne a garin Simon don kai kayan aikin da aka ba wa rundunar tsaron kasar Afirka ta Kudu wadanda aka ba umarnin a kai a shekarar 2018 daga kamfanin sayar da makamai na kasar Armscor," a cewar sanarwar.

Kwamitin ya kuma ce, "A game da kwangilar samar da makamai, kamfanin Armscor ko rundunar tsaron kasar Afirka ta Kudu ba su da wani iko wajen sauya hanyar da za a bi don kayayyakin su fita daga Afirka ta Kudu."

Fadar shugaban kasar ta ce zarge-zargen da aka yi wa Afirka ta Kudu na da illa ga tattalin arzikinta da kuma matsayinta a duniya.

Uzuri

"Afirka ta Kudu tana da kwararan dokoki da suka tsara yadda ake ba da izini game da shigo da makamai. Kuma sai da aka karba izini da ya dace a dukkan kayan aikin da jirgin ya kawo. Ba a ba da izini na fitar da makamai ba kuma ba a fitar da su ba,” in ji sanarwar.

Kwamitin binciken mai mutane uku ya hada alkali mai ritaya Phineas Mojapelo wanda ya jagoranci binciken da lauya Leah Gcabashe SC da kuma ’yar siyasa mai ritaya Enver Surty.

Sashen hulda da kasashen duniya da kuma hadin gwiwa na Afirka ta Kudu (DIRCO) ya fada a tsakiyar watan Mayu cewa jakadan Amurka Brigety ya nemi afuwa daga gwamnati da al'ummar Afirka ta Kudu kan kalaman da ya yi game da jirgin ruwan Rasha da ya lodo makamai da alburusai daga Afirka ta Kudu.

TRT Afrika