Asusun ko-ta-kwana na Ghana zai zuba jarin $33m a fannin hako ma'adanin Lithium a kasar kuma kasar za ta samu wani kaso na hannun-jari a Atlantic Lithium (A11.AX), kamar yadda kamfanin ya bayyana a ranar Juma'a.
Asusun adana kudi na Ghana's Minerals Income Investment Fund (MIIF) zai sayi kaso 6 cikin 100 na hannun-jari a kamfanin Atlantic Lithium a kasar ciki har da mahakar ma'adanai ta Ewoyaa, mahakar ma'adanin Lithium ta farko a yankin Yammacin Afirka a kan $27.9m, in ji wata sanarwa daga kamfanin Atlantic Lithium.
Zuba jarin wata manuniya ce kan yadda kamfanoni da ke samar da batura suke samun farin jini yayin da ake kokarin mayar da hankali wurin amfani da makamashi mara gurbata muhalli, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
A shekarar 2021, kamfanonin Piedmont Lithium (PLL.O) ya sayi kaso 9 cikin 100 na hannun-jari a kamfanin Atlantic Lithium don samun sinadarin Spodumene, abin da ya sa kamfanin ya kulla yarjejeniya da kamfanin da ke kera motoci masu amfani da lantarki wato Tesla Inc (TSLA.O).
Asusun MIIF zai sayi kaso 3.05 cikin 100 a kamfanin Atlantic Lithium a kan dala miliyan 5, a cewarsa.
Wannan zai ba shi damar neman sayen mahakar ma'adanai ta Ewoyaa wacce za ta rika samar da sinadarin Lithium.
"Akwai gogayya wajen fitar da ma'adanai wanda asusun MIIF zai shiga, amma bisa tsarin kasuwanci," in ji Shugaban Kamfanin Atlantic Lithium Neil Herbert.
"Akwai tsarin sarrafa sinadaran a kasa, akwai kamfanonin da ke samar da abubuwa daga tushe da wasu kamfanonin kasuwanci," a cewarsa.