Daga Nuri Aden
Ahmed Naji Sa’ad, fitaccen mawakin Somaliya ne wanda ya rasu a birnin Landan a ranar 6 ga watan Satumba yana da shekara 84.
Naji, wanda aka fi sani da Al Ustad, a hanyoyi da dama ya hada jiya da yau – inda ya yi wakoki tsawon shekaru wadanda suka hada da na kasa da siyasa da ci-gaba, inda matasa da dattawa duka suka san shi.
Mawakin ya rinka wa’azi kan zaman lafiya da sasanci haka kuma duk lokacin da ya samu damar yin waka domin karfafa gina kasa, ba ya kasa a gwiwa.
“Duka wadanda suka aika da sakon ta’aziyyarsu abu daya suke cewa – kan ba wai rashin uba kadai suka yi ba. Sun ji irin radadin da muke ji saboda su ma uba ne a gare su,” in ji Abdallah Ahmed Naji, wanda shi ne da na goma ga mawakin a tattaunawarsa da TRT Afrika.
“Abdirashid Mohamed, wanda marubuci ne dan kasar Somaliya, na kallon Naji a matsayin wanda ya hada kan kasarsa a lokacin da kasar ke bukatar waraka.
“Sauran mawaka a tsawon shekaru na kauna da kulla alaka a da shi. Ya taka muhimmiyar rawa wurin hada kan Somaliya, inda ya shiga tare da yin wasa a wurin tattaunawar da aka yi a Djibouti,” kamar yadda ya tuna.
“A lokacin tattaunawar, ya yi amfani da wakarsa wurin tuna wa shugabannin Somalia kan cewa kasar ya fi izza da son ransu girma. A daidai lokacin da ‘yan siyasa ke gardama, muryarsa ita ce ta sasanta su. Ya hada kan Somaliya ta hanyar kidan wakarsa duk da bakin bindiga ya raba su.”
Jinjina ga Turkiyya
A al’ada ta gaskiya ta mawaki wanda ba shi da iyaka, Naji ya shirya waka ta musamman wadda ya rera wa Shugaban Turkiyya Erdogan a lokacin da shugaban ya kai ziyara Somaliya a yayin da kasar ke fama da matsanancin fari.
A matsayinsa na shugaba wanda ba dan Afirka ba na farko da ya kai ziyara Somaliya a karon farko bayan yaki, Erdogan ya samu daya daga cikin yabon da ya ratsa zuciya daga daya daga cikin mawakan daga cikin mawakan da ake so. “Muna godiya a gare ka Shugaba Erdogan.
Gwamnatin Turkiyya da mutanenta sun bar mana tarihin da ba za mu manta ba. Sun kawo mana taimakon jin-kai, kuma ba za mu taba mantawa da hakan a zukatanmu ba,” haka baitocin wakar ke cewa.
Mutumin da ke da kwarewa daban-daban
Naji, wanda aka haifa a Somaliya a Mogadishu babban birnin Somaliya, ya iya harsuna iri-iri. Ya iya harshen Italiya da Larabci sosai.
A 1962, gwamnatin Somaliya ta gano irin basirar da yake da ita wanda hakan ya sa ta dauke shi a gidan rediyonta da ke Mogadishu.
“Lamari ne mai wahala a takaita irin gudunmawar da ya bayar ga Somaliya ko kuma yin bayanin girmamawa a gare shi,” in ji Mohamed Noor wanda ya yi waka tare da Naji. “Alakarmu da shi ta fara ne tun daga kan mahaifina, wanda ya ba shi jagorancin bangaren wake-wake a gidan rediyon Mogadishu.
Ya kasance furodusa mai basira iri-iri inda yake kaunar Somaliya. A lokacin yakin, tare da ‘ya’yansa, ya hada wata tawaga ta mawaka a Yemen domin ci gaba da fafutikar Somaliya.”
Komawarsa gida
Kafin ya koma gidan rediyon Mogadishu, Naji, yana wakoki da suka shafi ‘yanci da kuma gwagwarmayar neman ‘yanci da makadan Mogadishu na Shareero.
Abubuwan da ya gani daban-daban a kasar sun taimaka masa a wakarsa– tun daga lokacin mulkin mallaka zuwa bayan mulkin mallaka da mulkin soji da yakin basasan da aka jima ana yi da aka kawo karshensa bayan hakuri.
A tarihin Somaliya, Naji ya yi amfani da wakarsa da kuma tsananin fahimtar da yake da ita game da al’adar Somaliya domin kira ga hadin kan kasa, da dakile rabuwar kai da kabilanci, da kuma bayar da karfin gwiwa wurin soyayyar kasa.
Bayan shafe shekaru 20 yana zaune a kasar waje, komawarsa Somaliya a Disambar 2011 ta zama wani lamari na murna da nuna jin dadi a filin jirgin Aden Adde inda daruruwan ‘yan Somaliya suka tarbo shi.
Ko bayan samun mafaka a kasar waje bayan rugujewar gwamnatin Somaliya, Naji bai taba barin mutanen Somaliya ba ko rera musu wakoki ba a lokacin da ake rashin zaman lafiya.
Burin da bai cimmawa ba
Al'ummar Somaliya sun nun matukar nuna kauna da sha'awarsu marar iyaka.
Ga mutane da yawa, dawowar Naji ta wuce komawar sharararren mawaki zuwa mahaifarsa – komawarsa ta haifar da zaman lafiya a birnin da ya yi fama da abubuwa da dama.
“Naji ya koma Somaliya ba wai don ya ji dadin bazara a gefen tekun Indiya ba, amma don jagorantar farfado da wakokin Somaliya da kuma al’adunsu wadanda yaki da daidaita. Ya shirya taruka da horaswa da kuma tattakin wayar da kawuna a fadin kasar,” kamar yadda Abdirashid ya tuna.
Wasu daga cikin wakokin da suka saye zuciyoyi sun hada da Eebow Unukoo Nabadaa da kuma Gaarida Baarida Haween.
“Ya dauki wannan hanyar a sana’arsa ta waka saboda karfin gwiwar da ya samu na hasashen samun daidaitacciyar gwamnati a Somaliya, da kuma kasa wadda ‘yan uwa za su daina kashe junansu da hada kansu,” kamar yadda Abdalla Naji, wanda daya daga cikin ‘ya’yan Naji ne ya shaida wa TRT Afrika.
“Ya fi son zaman lafiya fiye da komai. Mahaifinmu ya yi mafarkin Somaliya ta yi karfi amma abin rashin jin dadi shi ne ba zai rayu ya gan ta ba.”
Kwarin gwiwa na tsawon shekaru
Naji ya samu kwarin gwiwarsa daga Qasim Hiwle da Mohamed Jama Joof, wadanda dukansu na daga cikin wadanda suka kirkiro wakokin Somaliya.
Haka kuma yana sha’awar Sufi Ali da Fatumo Hirad da Khadija Abdullahi Dalays. Shi ma ya bai wa mutane da dama kwarin gwiwa tsawon shekaru.
Zuwa lokacin samun ‘yancin kan Somaliya, Naji na cikin farkon shekarunsa na ashirin kuma ya samu daukaka cikin sauri.
Tun a baya, ya hada kai da mawaka daga arewa kamar su Abdullahi Qarshe da Aw Farah Dubbad da Ahmed Ali Haroun (Dararamle) da Osman Gacanlow da sauransu. Wasu daga cikin wadannan mutanen sun taimaka wa Naji ya wurin habaka wakokinsa.
“Mahaifina na son haduwa da masu basira. A duk lokacin da ya ga mawaka masu kyau, yana jawo su domin ya taimaka musu cike burinsu na zama mawaka,” kamar yadda Abdalla Naji ya tuna.
Zuciyar Somaliya
Shahararriyar mawakiyar nan ta Somaliya Maryan Mursal ta tabbatar da hakan.
“Naji ya taimaka mani samun aiki a lokacin gwamnatin Somaliya ta baya lokacin ina da da shekara 16. Na zama mawakiyar kasa kuma hakan ya faru ne duk sakamakon Naji Sa’ad wanda ya taimaka mani matuka,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Naji na daga cikin wadanda suka kirkiro kungiyar mawaka ta Waberi, wadda ta zagaye duniya. An ta kiransa domin gudanar da wasa a lokutan taruka na gwamnatoci a taruka irin na ranakun samun ‘yancin kai.
Ba abin mamaki bane mutuwar Naji da ta jefa Somaliya a cikin makoki.
Shugaba Hassan Sheikh Mohamud da Firaiminista Hamse Abdi Barre na daga cikin shugabannin da suka yi ta’aziyyar rasuwar mawakin ga iyalansa da kuma jama’ar Somaliya baki dayanta.
“Marigayin ya kasance zuciyar Somaliya a fannin waka, musamman kungiyar mawaka ta kasa ta Waberi,” kamar yadda wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa ta kasar ta fitar.
Shaharar da Naji ya bari a baya za ta ci gaba ta yaransa 16 wadanda wasu daga cikinsu mawaka ne. Sai dai dukansu sun tabbatar da cewa cike gurbin mahaifinsu zai dauki tsawon lokaci.