Babban Bankin Ghana ya fitar da rahotonsa kan asusun man fetur na ƙasar a watanni shida na ƙarshen shekarar 2024.
Rahoton ya nuna gagarumin ƙari a kuɗaɗen shiga na man fetur da ƙasar ta samu lamarin da ya janyo ƙari mai yawa a jarin da aka zuba a asusun man fetur ɗin Ghana zuwa dala biliyan 1.4, kamar yadda kammafin dillancin labaran Ghana ya ruwaito.
Rahoton ya ce ƙasar ta samu dala miliyan 543 daga ɗanyen man fetur da aka kwashe daga ƙasar a wannan lokacin.
Baya ga wannan, ƙasar ta samu ƙarin kuɗaɗen shiga daga harajin da kamfanonin mai suka biya da kuɗaɗen hayar filaye da kuma kuɗaɗen da ƙasar ta samu daga asusun adana kuɗin fetur na ƙasar wato Petroleum Holding Fund (PHF), lamarin da ya samar wa ƙasar fiye da dala miliyan 144.
Mafi yawa daga cikin dala miliyan 454 ɗin an saka su ne asusun man fetur na Ghana, Ghana Petroleum Fund, kuma aka tura dala miliyan 317 zuwa asusun adana kuɗin Ghana don gobe wato Ghana Heritage Fund kuma aka saka dala miliyan 136 cikin asusun ko-ta-kwana na ƙasar wato Ghana Stabilisation Fund.
Rahoton ya ce samu wannan muhimmin ƙarin ya sa kimar kuɗaɗen da ke cikin jerin asusun ya kai dala biliyan 1.4 zuwa ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2024.
Ya ƙara da cewa an ƙasafta kuɗaɗen a jerin asusun adana kuɗin Ghana don gobe wato Ghana Herita Fund da kuma asusun ko-ta-kwana ta ƙasar wato Ghana Stabilisation Fund ne bisa tsarin dokar sarrafa kuɗaɗen man fetur ta ƙasar wato Petroleum Revenue Management Act (PRMA).