Wata kotu a Accra babban birnin Ghana ta tura wasu 'yan Kamaru uku kurkuku bayan ta same su da laifin yunkurin mallakar fasfo da katin shaidar dan kasa na kasar domin samun damar tafiya Turai.
Alkaliyar Kotu Gundumar Madina da ke Accra Rosemary Abena Gyimah ta samu Tibab Beltus Mbachick, Mbaku Ransson da Mba Dieudonne Akuro da laifin karya dokar shiga-da-fice ta Ghana inda ta yanke musu hukuncin zaman wata daya a gidan yari.
Kazalika an ci tarar kowanne daga cikinsu cedi dubu hudu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana News Agency ya rawaito.
Alkaliyar ta ce mutanen za su sha daurin wata uku a gidan-maza idan suka gaza biyan tarar.
Mutanen uku sun amsa laifin yunkurin samun fasfo da katin dan kasa da takardar haihuwa na Ghana ta hanyar da ba ta dace ba da kuma shiga cikin kasar, har ma da zama a cikinta ba bisa ka'ida ba.