'Yan ƙasar Ghana na shirin zanga-zangar ne domin kokawa kan tsadar rayuwa. / Hoto: Reuters

Wata Babbar Kotu a Ghana ta hana ƙungiyoyin farar hula gudanar da zanga-zanga a Accra babban birnin ƙasar, kamar yadda ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar ya bayyana, inda suka bi sahun gwamnatocin kasashen Afirka wajen ƙoƙarin daƙile zanga-zangar da matasa ke yi kan tsadar rayuwa.

Waɗanda suka shirya zanga-zangar sun bayyana cewa zanga-zangar za ta jawo sama da mutum miliyan biyu a kan tituna domin neman Shugaba Nana Akufo-Addo ya ɗauki mataki kan cin hanci da rashawa.

Mai Shari'a Abena Afia Serwa ta amince da buƙatar 'yan sandan Ghana domin dakatar da wasu daga cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar daga gudanar da ita tsakanin 31 ga watan Yuli da kuma 6 ga watan Agusta bayan 'yan sanda sun bayyana cewa ba su da isassun jami'an da za su bayar da tsaro sakamakon an kai jami'an tsaron wuraren tarukan siyasa.

A halin yanzu ana fama da guguwar zanga-zanga wadda ke kaɗawa a faɗin ƙasashen Afirka a 'yan makonnin nan.

Zanga-zangar Kenya da Uganda

A Kenya, sama da mutum 50 aka kashe inda kuma aka kama sama da 700 a yayin da 'yan sanda suka yi dirar mikiya kan masu zanga-zanga tun daga tsakiyar watan Yuni, a lokacin da masu zanga-zanga suka soma fantsama kan tituna inda suke adawa da tsarin haraji wanda Shugaba William Ruto ya gabatar, kamar yadda Hukumar Kare Haƙƙin Bil'adama ta Kenya ta bayyana.

Ruto ya sallami ministocinsa tare da dakatar da kudirin ƙara harajin.

A makon da ya gabata, matasa a Uganda sun fantsama a kan tituna inda suke zanga-zanga kan zargin cin hanci da rashawa da kuma neman kakakin majalisar ƙasar ya yi murabus.

Zanga-zangar Nijeriya da aka shirya

A yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a Nijeriya, gwamnatin Nijeriya ta sanar da ɗaukar aiki a kamfanin mai na ƙasar NNPCL da kuma bayar da tallafi na biliyoyin nairori domin sanyaya gwiwar matasa kan fita zanga-zangar da suke shirin somawa kan tsadar rayuwa.

A Ghana, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya zanga-zangar Mensah Thompson ya bayyana cewa bai kamata a ce zaɓe ya dakatar da 'yan ƙasa daga gudanar da zanga-zanga ba wadda 'yancinsu ce a matsayinsu na 'yan ƙasa.

"Matasa sun shirya gudanar da zanga-zanga tare da amincewa ko kuma rashin amincewar hukumomi," in ji shi.

"Lokaci zai zo wanda za su hau kan tituna inda za mu samu zama kamar Kenya."

Matsalar bashi a Ghana

Tattalin Arzikin Ghana ya tabarbare bayan sakamakon irin jerin basussukan da ta ci a shekarun baya da kuma annobar korona, da kuma irin tasirin da yaƙin Ukraine ya yi a ƙasashen duniya.

Ƙasar ta Ghana wadda ke samar da koko da zinare na ta ƙoƙarin yadda za ta samu rangwame wurin biyan bashinta na ƙasashen waje na dala biliyan 30 domin samun wasu kuɗin tallafi na biliyan uku daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya don farfaɗowa da tsananin matsin tattalin arziƙin da suke fama da shi.

A watan Disamba ne za a gudanar da babban zaɓen ƙasar Ghana da zaben 'yan majalisa da kuma wanda zai gaji shugaban ƙasar mai ci a yanzu Nana Akufo-Addo.

TRT Afrika