Wani mai sharhi kan tsaro ya ce hukuncin kotun ya nuna cewa Ghana na bunkasa a matsayin kasa mai bin cikakkiyar dimokradiyya/Photo Getty

Wata Babbar Kotu a birnin Accra na Ghana ta yanke wa wasu mambobin haramtacciyar kungiyar aware da ke fafutukar ballewar kasar Togoland hukuncin daurin shekara biyar-biyar a gidan yari da kuma aiki mai tsanani.

Wannan ne hukunci na farko da aka yanke wa wasu mutane bisa hannu a harkokin da suka shafi 'yan aware a kasar, wacce take Yammacin Afirka.

Masu laifin, wadanda dukkan su mambobin kungiyar 'yan aware ce ta Western Togoland Restoration Front, na daga cikin gomman mutanen da aka kama a shekarar 2020 kan laifin kai wa ofisoshin 'yan sanda hari.

A lokacin da suka kai hare-haren sun kuma saki masu laifi da ake tsare da su da kona ababen hawa na jami'an tsaro da kuma toshe wata babbar hanya.

Daga baya an saki wasu daga cikin wadanda ake zargin bayan da hukumomi suka tantance su. Amma an ci gaba da tsare biyar din da aka yanke wa hukunci a wannan Talatar.

Kafafen yada labarai na kasar Ghana sun ruwaito cewa lauyan 'yan awaren da aka yanke wa hukuncin ya nemar wa wadanda yake karewan sassauci.

Ghana na daya daga cikin kasashen Afirkan suka fi zaman lafiya. Amma wasu kungiyoyi a yankunan Volta da Oti sun shafe shekaru suna ta fafutukar ballewa. Sai dai fafutukar ta kasance cikin lumana har sai a shekarar 2020 sannan ra zama kamar rikici.

Wani mai sharhi kan tsaro Irbad Ibrahim, ya ce hukuncin kotun ya nuna cewa Ghana na bunkasa a matsayin kasa mai bin cikakkiyar dimokradiyya da ake biyayya ga dokoki.

Ya ce a shekarun da suka wuce a kan yanke wa 'yan aware hukunci ne yawanci ta hanyar bindige su kan laifukan cin amanar kasa.

Mr Irbad ya ce, amma wannan hukuncin na yanzun ma zai zama "gargadi ga sauran mutanen da ke neman wargaza zaman lafiyar Jamhuriyyar Ghana."

Amma ya shawarci hukumomin Ghana da su sake yin duba kan korafe-korafen 'yan awaren da suka hada da rashin ci gaba a yankinsu ta hanyar "kawo tsari na yin maraba da kowa."

TRT Afrika