Samuwar intanet har yanzu tana da karanci a Afirka /  Hoto: AP archive

Daga Gaure Mdee

Ranar 7 ga watan Fabrairu, Ministan Sadarwa na Tanzania, Nnape Nauye ya amsa wani sakon Twitter daga mai kamfanin na Twitter, wato Elon Musk dangane da yadda Tanzania ta karbi Kamfanin Starlink mai samar da intanet ta tauraron dan’adam.

Za a iya yin tambayoyi da yawa kan wannan tattaunawa ta Twitter. Da farko, me ya sa kamfanin na Elon Musk da ke amfani da fasahar (VSAT) yake janyo hankalin mutane duk da cewa ba wani sabon abu ya zo da shi ba.

Na biyu shi ne mece ce kimar kasuwancin samar da intanet ta amfani da tauraron dan’adam, wanda har take janyo neman wannan amsa?

Sai kuma a karshe, me ya sa irin wadannan tattaunawa tana wakana a kafar sada zumunta, maimakon a kafa mafi dacewa, ko dai tattaunawar ta wuce nan?

Mene ne batun?

Don mu fahimci abin, kashi 26% na mutanen gabashin Afirka suna da hadin intanet, bisa wani bayani na shafin Statista na shekarar 2022.

Mutane a yankunan karkara suna da karancin samun intanet sama da na biranen a Afirka. Kafin ka iya mallakar Starlink ya yi aiki, dole ka fara duba yankunan da kamfanin na Elon Musk ke fatan cimmawa.

Baya ga batun samun lantarki da arzikin iya sayen na’urar, shin mutane sun shirya saya da dasa wannan na’ura a farashin da ake sayar da ita yanzu?

Starlink suna sayar da giga 1,000 GB na intanet mai karfin 20ms da saurin 150Mbps a kusan kasa da dala 100 a Tanzania, farashin da ya fi kowanne kamfani a kasar.

Bugu da kari, suna shirin fara samar da sadarwar waya mai amfani turakun sadarwa mai aiki da tauraron dan’adam, wanda zai janyo kamfanonin cikin gida sai sun nemi taimako kafin iya gasa da shi.

Amma akwai wani kandagarki, kudin kayan aikin da kuma aikin kafa shi wanda akan biya sau daya, yana da tsada. Ga misali, idan ana samun sauyin yanayi.

A irin wannan yanayi, karfin sabis din yakan tabu, tamkar yadda kake gani idan kana kallon tashar Multichoice lokacin da ake mamakon ruwan sama.

“Kamfanin Elon Musk bai zo da wani sabon abu ba, kawai dai yana da alfanun kasancewa mai saukin farashi a irin kasuwar, kuma ana kafa shi a farashi mai sauki.

Masanin kasuwancin intanet kuma mai fafutukar kare jama’a, Jumanne Mtambalike, ya ce, “An zuba kudi a kamfanin idan aka kwatanta da masu gogayya da shi, wadanda suka yi kokarin hada sadarwa a Afirka ta amfani da salo iri daya.”

Kamfanonin sadarwa na cikin gida a yankin, kamar su Safaricom na Kenya da Tigon a Tanzania sun fara fito da sabuwar fasahar 5G, mai saurin 500Mbps. Kuma ba ya nisan zango sai an saka rauta.

Mutane da suka saba amfani da nau’rar VSAT su ne masu kamfanonin wuraren bude ido, da masu bincike a daji, da jami’an tsaro da ke sa ido kan mutane da suke bibiya.

Wadanne tsare-tsare ake akwai da su?

Masu samar da intanet ta amfani da tauraron dan adam suna iya samun kudi daga kusa da nesa, kuma suna daukar ma’aikata ‘yan kadan don gudanar da kamfanin.

Starlink yana cikin manyan kamfanoni masu samar da intanet a Tanzania. Hoto: Reuters Archive

Kamfanin ya hada gwiwa da kungiyar Sadarwar Tarho ta Afirka, “African Telecommunications Union (ATU)”, don saukaka kaddamar da kamfanin Starlink a Afirka.

ATU wata kungiyar Afirka ce da ta hado kasashe da kamfanoni sadarwar tarho don kara gina harkar sadarwa da fasahar kayayayakin sadarwa a Afirka.

Tarayyar Afirka tare da ATU sun fito da wani tsari saka idon da ya ba da dama ga kamfanin Starlink ya fara aiki da tararon dan’adam dinsa don samar da inatent a fadin kasashen Afirka.

Akwai kyakkyawan dalilin da kasashen gabashin Afirka za su yi adawa da Starlink, kuma su ci gaba da amfani da kamfanon sadarwa na cikin gida.

Zai yiwu gwamnatocin da ba su riga sun rungumi fasahar ba saboda sun duba barazanar da shigo da su kasarsu zai yi kan kamfanonin cikin gida, musamman kan daukar ma’aikata.

Jumanne Mtambalike, wani masanin sadarwa a Afirka

Ta la’akari da cewa da yawa daga cikinsu suna samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa, kuma suna bin dokokin kasashen, kuma suna bin umarni da ikon gwamnatocin kasashen.

Jumanne Mtambalike, wani masanin sadarwa a Afirka ya ce, “Zai yiwu gwamnatocin da ba su riga sun rungumi fasahar ba saboda sun duba barazanar da shigo da su kasarsu zai yi kan kamfanonin cikin gida, musamman kan daukar ma’aikata."

Wurare masu nisa wadanda ba su da kayan more rayuwa za su samu cigaba a harkokin intanet. Akwai da dama da ba su da wutar lantarki, amma wannan din za ta kai gare su.

Sai dai wannan zai iya janyo kalubale ga kamfanonin sadarwa na cikin gida, da kuma gwamnatin Tanzania.

Duk wanda ya fara cimma daidaiton samar da aiki, shi zai yi nasarar samun kwastomomi. Idan yankin ya zabi kwafar gwamnatocin baya, ba da lasisi ga kamfanin intanet mai amfani da taruraron dan’adam zai gamu da wasu dokokin iyakancewa.

Jumanne Mtambalike wani mai kasuwancin inatnet, yana ganin Elon Musk yana da wani fifiko sama da sauran kamfanoni saboda yawan kudin zuba jari da yake da shi. Hoto: Jumanne

Wani babban mislai shi ne a zaben Uganda da aka yi kwanan nan a 2021 da kuma zaben Tanzania na 2020.

An gi yadda aka kashe intanet yayin zabukan, wanda ya durkusar da kamfanoni kuma ya rufe bakin masu fallasa.

Abin da mutanen da suke amfani da wannan fasaha a halin yanzu suke cewa. Wani abu da zai faru ba a tsarin samar da intanet da sauran ayyukan sadarwa, na tauraron dan adam.

Nijeriya daya ce daga kasashen Afirka na farko da suka rungumi tsarin da Starlink ya zo da shi, tuna a watan Janairu.

Kabir Ibrahim, wani injiniyan sadarwa ne a Nijeriya. Ya fada wa TRT Afrika cewa “Yawancin ‘yan Nijeriya za su ga tsadar Starlink wajen sayen kayan da kuma biyan kudin shiga tsari. Amma da zarar akwai alfanu ga rukunin mutane kamar iayali a gida.”

Tun kaddamar da shi a Rwanda ranar 22 ga Fabrairu, yawancin masu aiki da shi daga bangaren gwamnati suke.

TRT Afrika ta tattauna da wani dan jaridar kasar Rwanda, Johnson Kanamujire, wanda ya halarci taron kaddamar da shirin.

Ya ce, “A yanzu ba za a iya gane ko zai samu karbuwa ba. Amma da alama, ana nufin cimma ofisoshin gwamnati da makarantu da yankuna masu nisa, da tsibirai, da yankunan karkara da ba su da intanet.”

A wani bangaren, kasar Kenya za ta fara amfani da kamfanin a karshen shekarar nan, duka da farashin na’uarra ya kai dala 800.

Moses Kemibaro, wani masanin fasaha a Nairobi ya sanar da TRT Afrika cewa ya saka odar siyar na’urar don “ya gwada ta”.

Yana so ya gane ko wannan zai zama madadin sauran tsarin samun intanet da ya saba da su.

“Yawan yankewa sabis da katsewar sauri aiki shi zai sa mutum ya ci gaba da amfani da tsarin intanet ta wayan hannu.”

Jinjirin da kasashe ke yi kamar su Tanzania a halin yanzu, wata alama ce babba. Duk da za a samu kudi sosai daga gwamnati, amma akwai yiwuwar samu tarnakin amfani.

Starlink daya ne daga cikin kamfanoni masu samar da intanet, amma ba shi ne ya fi sauki ba.

Yayin da kamfanoni kamar Microsoft suna shirin shiga samar da intanet a kasashe masu tasowa, abin tambaya shi ne ko yankin ya shirya karbar wannan sabon tsari?

TRT Afrika