Shugabar hukumar ta ARCEP ta ce tun 2021 ta ja hankalin kamfanonin a kan kasawarsu wajen inganta harkar sadarwa a fannin kiran waya da kuma internet. Hoto: OTHERS

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ci tarar kamfanonin wayar sadarwa hudu kudi sama da CFA biliyan hudu sakamakon kasawa wajen inganta ayyukansu a wasu yankuna na kasar.

Kamfanonin sun hada da CELTEL NIGER MOOV da AFRICA NIGER NIGER TELE.COM da kuma ZAMANI TELE.COM.

Hukumar da ke sa ido kan ayukan kamfanonin waya ta kasa ARCEP ce ta sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai da shugabar hukumar Mme Betty Aichatou Habibou Oumani ta jagoranta a ranar Litinin.

Shugabar hukumar ta ARCEP ta ce tun 2021 ta ja hankalin kamfanonin a kan kasawarsu wajen inganta harkar sadarwa a fannin kiran waya da kuma internet.

Hukumar ta ce binciken da kwararrunta suka gudanar ya gano cewa wasu garuruwa na jihohi bakwai daga cikin takwas na kasar ne ke fama da wannan matsalar ta rashin ingancin sadarwar wayoyi.

Hukumar ta ce baya ga cin kamfanonin wannan tarar ARCEP din ta ce a nan gaba duk kamfanin da ya kasa gyara kura-kuransa to akwai yiyuwar a dakatar da shi na wani lokaci koma ta kai ga amshe lasisin kamfanin.

TRT Afrika