Ta ce abun "ba shi da wata barazana ga tsaro a yanzu". Hoto / KBC

Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Kenya a ranar Juma'a ta ci gaba da binciken wani katon ƙarfe da ya fada a kasar a farkon makon nan.

Hukumar ta ce, a ranar 30 ga watan Disamba, wani zagayayyen ƙarfe mai kusan kafa 8 (mita 2.4) mai nauyin kilo 1,100 (kimanin kilogiram 453) ya fado kauyen Mukuku da ke gabashin gundumar Makueni daga sama, in ji hukumar.

"Sakamakon binciken farko ya nuna cewa abin da ya fado ƙarfe ne da ya balle daga jikin wata roka da aka harba," in ji hukumar yayin da ake ci gaba da gwada abun.

Ta ce abun "ba shi da wata barazana ga tsaro a yanzu" kuma tana kokarin tantance ainihin asalinsa.

'Har yanzu da zafinsa'

Lokacin da wata tawaga daga hukumar da jami'an yankin suka isa wurin a ranar Litinin, sun "samu ƙarfen da sauran zafi a jikinsa," a cewar Julius Rotich, wani jami'in 'yan sandan yankin.

Rotich ya shaida wa kafar yada labarai ta kasar Kenya, cewa ‘yan sanda sun killace wurin har sai abin ya yi sanyi.

AA