Gwamnatocin Kenya da Uganda sun ja hankalin al’ummominsu game da matakan da suka kamata su dauka wajen kare kansu daga cutar Marburg kwanaki kadan bayan Tanzania ta sanar da barkewar cutar a kasarta.
Cutar ta barke ne a arewa maso yammacin Tanzania inda ta yi sanadin mutuwar akalla mutum biyar.
Uganda na shirin aikewa da kwararru zuwa yankunan Kasensero da Mutukula da ke makwabtaka da Tanzania.
Ma’aikatar Lafiya ta Uganda ta sanar a ranar Alhamis cewa za ta aika tawagar kwararru domin yin gwaji kan mutanen da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakar Uganda da Tanzania da zummar ganin ba a shiga da cutar kasar ba.
A wata sanarwa da ya aike wa shugabannin larduna, Darakta Janar na hukumar kula da lafiyar kasar, Dr Henry Mwebesa, ya umarce su da su rika sanya idanu a kan masu tsallakowa cikin kasar da makwabtan kasashe domin tabbatarwa ba a shigo da cutar ba.
‘Tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama’
Kasar Kenya da ke makwabtaka da Tanzania ta bayyana cewa za ta gudanar da gagarumin aikin tantance bakin da ke shiga kasar.
A wani sakon Tuwita da Ma’aikatar Lafiyar kasar ta wallafa, ta ce gwamnati za ta sanya ido a tashar jiragen ruwa ta Bukoba da kuma filayen jiragen sama.
A halin da ake ciki babu allurer riga kafin cutar Marburg.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da kwararru yankin Kagera domin gudanar da bincike.