Shugaban kasar Uganda ya sanya hannu kan dokar kyamar masu auren jinsi wadda mutane suke goyon baya sosai a kasashen Gabashin Afirka.
Bangaren dokar da Shugaba Yoweri Museveni ya sanya wa hannu bai hana mutane su ayyana kansu a matsayin masu auren jinsi daya ba.
Amma sabuwar dokar ta amince a zartar da hukuncin kisa “ 'yan luwadi,” wadanda aka bayyana a matsayin masu yin tarayya da mutanen da ke dauke da cutar HIV, da kananan yara da mutanen da ke da rauni.
Duk mutumin da aka kama da laifin aikata “luwadi” zai iya shan daurin da ya kai shekara 14, a cewar dokar.
Shugabar Majalisar Dokokin kasar Anita Among ta fitar da sanarwa inda ta c shugaban kasar ya “amsa kiraye-kiraye da 'yan kasarmu”.
TRT Afrika da abokan hulda