Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar daya ga watan Yuni ne ofishin kiwon lafiya na yankin Upper East ya samu labarin bullar cutar anthrax Hoto/AA

Daga Mazhun Idris

A Ghana, bayan tabbatar da mutuwar mutum guda saboda cutar anthrax, da kuma kamuwar mutane sama da goma cikin al’ummar yankin Binduri na gabashin kasar, gwamnati ta sanar da haramta cin naman dabbar da cutar da kama.

Ministan Abinci da Noman na Ghana, Bryan Acheampong ya sanar da haramta cin naman dabbobi da suka mutu bayan kamuwa da cutar a yankunan da cutar ta addaba, wato lardin Binduri da ke yankin Upper East Region.

Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar daya ga watan Yuni ne ofishin kiwon lafiya na yankin Upper East ya samu labarin bullar cutar anthrax.

An kuma samu labarin rasuwar mutum guda da ya ci naman saniyar da ta kamu da cutar. Shanu hudu ne suka mutu a yankin da cutar ta shafa.

Hanyoyin kariya daga anthrax

TRT Afrika ta nemi jin ta bakin wani kwararren likita, Dr. Sule Ali Gabas, wanda ke Sagmediconsult and Diagnostic Services Ltd, a Accra, babban birnin kasar. Likitan ya ce, “Kwayar cuta mai suna Bacillus anthracis ita ke haifar da cutar anthrax, kuma an fi ganin cutar ne a dabbobi kamar shanu ko tumaki.”

Mutane sukan iya kamuwa da cutar anthrax sakamakon mu’amala da dabbar da ke dauke da kwayar cutar, ta hanyar cin nama ko shan nonon dabbar, ko ta hanyar kusanata ko taba dabbar, ko kuma shakar kwayar cutar cikin iska.

Dr. Gabas ya kara da cewa, “Aalamun cutar suna da dama, hudu daga cikinsu su ne fatar jiki ta fara kaikayi, har kurji ya fito mara zafi. Sai kuma zafin jiki, da ciwon kai da kuma ciwon ciki. In dai kwayar cutar ta shiga jiki, to za a ga alamunta cikin kwana shida.”

“Amma wadanda suka harbu da cutar ta hanyar numfashi, za su iya haura kwanaki shida kafin bayyanar alamar cutar, wanda kan kunshi mura, da ciwon makoshia, da yawan gajiya, da ciwon kirji da gabobi, da kuma tashin zuciya, har ma da tari da zai iya zuwa da jini”.

Cutar anthrax da aka dauka ta numfashi tana da muni kwarai, kuma yayin da kwayara cutar ta kai ga kwakwalwa, takan iya haifar da cutar sankarau.

Matakan kariya daga cutar anthrax

Cutar anthrax da ake samu daga cin naman dabbobi takan nuna alamu kamar ciwon ciki, amai, tashin zuciya, ciwon kai, da gudawa mai zuwa da jini.

Dr. Gabas ya bayar da wasu shawarwarin da za su taimaka wajen kaucewa wannan cuta.

  • Nisanta mu’amala ko taba dabbobin da suka kamu
  • Kauracewa nama ko nono ko duk wani abu da ya fito daga dabba mara lafiya
  • Daina shiga yankin da cutar ta bayyana har sai an shawo kanta
  • Garzayawa asibiti idan an fuksanci alamu ko barazanar cutar.

Haka nan, ita ma gwamnatin Ghana ta sanar da daukar matakan shawo kan yaduwar cutar zuwa sauran sassan kasar, domin kare lafiyar jama’a. Daga cikin matakan akwai:

  • Takaita zirga-zirgar dabbobi a yankin da kuma tsakanin yankan da cutar ta bayyana
  • Shirin yin rigakafin anthrax kan dabbobi a yankuna da cutar ta fara yaduwa
  • Dokar haramta cin naman dabbar da ta kamu ko ta mutu sakamakon cutar
  • Gaggauta kai rahoton mutuwar dabba zuwa asibitin dabbobi.

A karshe dai, Dr. Sule Gabas ya shawarci jama’a da su san cewa wadannan matakan za su taimaka wajen ba su kariya, da kuma saukaka magance yaduwar cutar a Ghana.

Ya kuma kara da cewa athnrax cuta ce da ake iya yin maganinta, har a samu waraka musamman idan an dauki matakin zuwa asibiti kan lokaci.

TRT Afrika