Kasashe 10 sun gabatar da wani koke a gaban Kotun Kasa da Kasa ta Duniya wato International Court of Justice (ICJ) a birnin Hague, dangane da karar da Afirka ta Kudu ta shigar kan kisan kiyashin da Isra’ila ta yi da batun mamaye Gaza wanda ya saba wa doka.
Masanin shari’a dan kasar Belgium Vaios Koutroulis ya yi Allah wadai game da amfani da karfi a kan Falasdinawa kuma ya bukaci Isra’ila ta kawo karshen hakan ta hanyar mutunta dokoki, sannan ya ce ya kamata a hukunta wadanda suka aikata laifin.
Kazalika ya ce tsare-tsaren Isra’ila suna da aniyar canja tsarin zamantakewa a yankunan Falasdinawa.
Wakilin kasar Belize Assad Shoman ya ce Falasdinawa suna da hakkin zaba wa kansu makoma da kuma ’yancin kasancewa, wadannan hakkoki ne da Isra’ila ta take musu.
Jakadaan Bolivia a kasar Netherlands Roberto Calzadilla Sarmiento ya ce mamayar da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa ta saba wa dokokin kasa da kasa.
Wakiliyar kasar Brazil Maria Clara Paula de Tusco ta ce tana so kotun ta jaddada cewa mamayar da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa ya saba wa ka’ida da dokokin kasa da kasa.
Wakiliyar Chile Ximena Fuentes Torrijo ta ce da halin Falasdinawa suke ciki a yankunansu da Isra’ila ta mamaye, za a iya warware shi cikin adalci ne kawai idan aka yi amfani da mafitar da Majalisar Dinkin Duniya ta shata da dokokin kasa da kasa da kuma dokokin jin-kai na duniya.
Matsayar Isra’ila ta ci karo da tanade-tanaden warware matsalar ta hanyar samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin, in ji ta.
Kasashen Afirka ta Kudu da Aljeriya da Netherlands da Bangladesh duka suna da wakilci a Kotun ICJ.
An fara sauraren karar ne a ranar Litinin a birnin Hague biyo bayan wata bukata ta Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya kan abubuwan da ka je so zo kan tsare-tsare da manufofin Isra’ila a yankunan Falasdinawa da ta mamaye ciki har da Gabashin Birnin Kudus
Afirka ta Kudu ta shigar da karar Isra’ila a Kotun ICJ a karshen watan Disamba kuma ta bukaci a samar da wasu matakai na gaggawa don kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Gaza, inda aka kashe fiye da Falasdinawa 29,000 tun bayan fara rikici a ranar 7 ga watan Oktoban bara.
Kotun a watan Janairu ta bukaci Isra’ila da ta yi “dukkan mai yiwuwa” ta kiyaye faruwar kisan kiyashi a Gaza, sai dai ba ta umarce a tsagaita wuta ba.
Kotun ta umarce Isra’ila ta dauki matakai “nan take” don samar kayayyakin gaggawa da na jin-kai a Gaza.
Kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta kai hari a cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,200, amma martanin da Isra’ila ta mayar a Gaza ya yi sanadin kaso 85 cikin 100 na mutanen yankin sun rasa muhallinsu, inda suke fuskantar matsalar karancin abinci da ruwa mai tsafta da magunguna yayin aka lalata gine-gine kaso 60 cikin 100 a yankin, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke yi, yanzu Isra’ila tana shirin kai farmaki ta kasa a Rafah, inda ake da ’yan gudun hijira kimanin miliyan daya da dubu 400.