Maleriya wadda sauro ne ke bazata, na kashe kusan mutum 600,000 a duk shekara. / Hoto: AA

Kamaru za ta kasance kasa ta farko da za ta saka rigakafin cutar maleriya a cikin jerin alluran rigakafin yara.

Shirin wanda ake sa ran farawa a ranar Litinin, hukumomi sun bayyana shi a matsayin wani babban ci gaba bayan shafe shekaru aru-aru ana kokarin dakile cutar wadda sauro yake bazawa a nahiyar. “Wannan rigakafin zai ceto rayuka.

"Zai kawo babban taimako ga iyalai da kuma bangaren kiwon lafiya na kasa,” in ji Aurelia Nguyen, wadda ita ce shugabar shirye-shirye a kungiyar the Gavi Vaccines Alliance, wadda kungiya ce da ke taimaka wa Kamaru samun rigakafin.

Kasar wadda ke a tsakiyar Afirka na sa ran yi wa yara 250,000 rigakafi a bana da shekara mai zuwa.

Gavi ta bayyana cewa a halin yanzu tana aiki tare da kasashen Afirka 20 domin taimaka musu samun rigakafin da za su yi wa sama da yara miliyan shida har zuwa 2025.

Adadin da ake bukata

A Afirka, akwai kusan matsaloli kusan miliyan 250 na cututtuka wadanda ake samu daga sauro da sauran dabbobi inda ake samun kusan mutum miliyan 600 da ke mutuwa kuma akasarinsu yara.

Kamaru za ta yi amfani da rigakafi biyu na farko da aka amince da su wadanda aka fi sani da Mosquirix.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da wannan rigakafin shekara biyu da ta wuce, inda ta ce duk da cewa bai cika dari bisa dari ba amma za ta rage matsalolin da ake da su matuka na kamuwa da cutar da kwantar da mutane a asibiti.

Allurar GlaxoSmithKline tana aiki ne da kusan kashi 30 cikin 100, inda ana yin ta har sau hudu, sai dai kariyar tana tafiya bayan watanni da dama. An yi gwajin cutar a Afirka inda aka yi a kasashe uku. Masana sun ce baya ga rigakafin, akwai wasu kayayyaki da suka hada da gidan sauro da maganin fesawa na sauro wadanda ake tsananin bukata. Cutar ta maleriya idan ta yaɗu akasari tana jawo masassara da ciwon kai da jin sanyi.

AP