Salama Marouf, ta ce "duk da kwanaki 20 da suka wuce da yarjejeniyar, halin da ake ciki na jinƙai na ci gaba da yin muni. Hoto: Reuters Archive

1254 GMT — Hukumomi a Gaza sun sanar da cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da tanade-tanaden jinƙai na yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu.

Da take magana a wani taron manema labarai a asibitin al-Ahli Arab da ke birnin Gaza, shugabar ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza Salama Marouf, ta ce "duk da kwanaki 20 da suka wuce da yarjejeniyar, halin da ake ciki na jinƙai na ci gaba da yin muni mai tsanani saboda hanin da Isra'ila ta yi."

Ta yi bayanin cewa "yarjejeniyar ta tanadi shigar da manyan motocin agaji 600 a kullum, ciki har da manyan motocin mai 50, tare da samar da gidajen kwana 60,000 na tafi da gidanka da tantuna 200,000 da janaretoci da kayayyakin gyara da na'urorin hasken rana, da kayayyakin sake gina Gaza."

Ya kara da cewa, "yarjejeniyar ta kuma hada da kawar da tarkace da gyara wuraren kiwon lafiya da gidajen burodi, da ababen more rayuwa, da tabbatar da zirga-zirgar marasa lafiya da wadanda suka jikkata ta hanyar Rafah."

0410 GMT — Biyu bisa uku na wuraren kiwon lafiya na Gaza ba sa aiki — WHO

Babban jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya na Gaza ya ce asibitoci 18 daga cikin 36 ne kawai ke aiki a wani bangare kuma 57 daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya na farko 142 ke aiki.

Daga tsakanin 1 ga Fabrairu zuwa 5 ga Fabrairu, an samu raunuka 139 da marasa lafiya da aka kwashe daga Gaza zuwa Masar ta mashigar Rafah, in ji Dr Rik Peeperkorn.

Ya ce har yanzu akwai buƙatar kwashe majinyata 12,000 zuwa 14,000 ciki har da yara 5,000 - kuma a yadda ake tafiya, kwashe likitocin zai dauki shekaru biyar zuwa 10 kuma marasa lafiya masu fama da cutar za su mutu.

0226 GMT — Ministan Harkokin Wajen Jordan zai ziyarci Washington domin tattaunawa kan Gaza

Kamfanin dillancin labaran Axios ya bayar da rahoton cewa, Ministan Harkokin Wajen Jordan, Ayman Safadi, zai ziyarci Washington domin ganawa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio da wasu jami'an gwamnatin Trump.

Sarki Abdallah na biyu na kasar Jordan ya fara wani balaguro zuwa ƙasashen duniya a ranar Alhamis domin ganawa da jami’ai a Birtaniya da Amurka, ciki har da Shugaban Amurka Donald Trump.

Rahoton ya ce ziyarar ta Safadi na zuwa ne gabanin ganawar da Sarki Abdullah zai yi da Trump a fadar White House ranar Talata.

2200 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a Lebanon, ta saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a kudanci da gabashin kasar Lebanon tare da shawagi a babban birnin kasar Beirut da kewayen birnin, lamarin da ke nuna saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Jiragen yakin kasar sun kai hari a wani yanki na gabashin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Labanon (NNA) ya ruwaito.

TRT Afrika da abokan hulda