RSF

Rundunar RSF ta Sudan ta sanar da tsagaita wuta na kwana biyu albarkacin hidimar Babbar Sallah.

"Mun ayyana tsagaita wuta daga bangarenmu, sai dai a yanayi na kare kai, a jajiberin sallah da kuma ranar Babbar Sallar," in ji Kwamandan RSF, Mohammed Hamdan Dagalo.

Ya sanar da hakan a wani sakon murya da aka nada aka kuma wallafa a shafin Facebook ranar Litinin.

Ana sa rana za a tsagaita wutar ne a ranakun Talata da Laraba, amma har yanzu rundunar sojin Sudan ba ta ayyana matsayarta ba.

Shugaban rundunar ta RSF na fatan lokacin hutun sallar zai samar da damar sasantawa a tsakanin al'ummar Sudan.

An amsa addu'a?

Mahajjatan Sudan da ke gudanar da Aikin Hajji a Makkah na addu'ar fatan samun zaman lafiya a kasarsu.

Sanarwar shugaban RSF ga alama addu'a ce ta fara karbuwa, da har aka fara tsagaita yakin da aka shafe wata kusan uku ana yi.

Hukumar Kula da Masu Kaura ta (IOM) ta Duniya ta yi kiyasin cewa yakin da ake yi tsakanin rundunar sojin da RSF ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 2,000 tare da raba mutum miliyan 2.5 da muhallansu.

An sha sanar da tsagaita wuta a bata, amma duk ba su yi aiki ba. Bangarorin biyu da ke yaki da juna suna zargin juna da lalata yarjejeniyoyin.

Da yake magana kan halin da ake ciki dalilin yakin, Dagalo ya ce: "Muna fatan mu magance matsalar nan tare da hada kai da sake yin karfi."

TRT Afrika da abokan hulda