Rundunar sojojin sama ta Nijeriya ta ce jiragen yaƙinta sun yi luguden wuta a sansanoni uku na ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da lalata maɓoyarsu ranar Laraba.
Kakakin rundunar sojojin saman ta Nijeriya, AVM Edward Gabkwet, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis, ya ƙara da cewa dakarunsu na rundunar Operation Hadarin Daji ne suka aiwatar da wannan gagarumin aiki.
Gabkwet ya ƙara da cewa sansanonin da aka yi wa luguden wuta na fitattun ƴan ta'adda ne -- Abdullahi Nasanda a Zurmi, da Malam Tukur a Gusau, da kuma wani sansani a ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
Kakakin rundunar sojojin saman ta Nijeriya ya ce jami'ansu sun yi amfani da na'urori na leƙen asiri a sansanin ƴan ta'adda na Nasanda inda aka hango ƴan ta'adda suna kai-komo kuma sun ɓoye baburansu.
“Bayan an tabbatar da ayyukan da suke yi irin na ƴan ta'adda, sai jirage suka yi luguden wuta a sansanonin inda suka kashe ƴan ta'adda da dama.
“Kazalika an gudanar da irin wannan leƙen asiri a sansanin Malam Tukur inda aka ga ƴan ta'adda suna kazar-kazar. Daga nan aka kai musu hari inda aka kashe da yawa daga cikinsu sannan aka lalata sansaninin," in ji sanarwar.
“Haka kuma an kai hare-hare ta sama a Kanikawa da ke garin Maradun, a ƙaramar hukumar Maradun da ke Zamfara, inda aka kashe ƴan ta'adda tare da lalata maɓoyarsu da kayan aikinsu," a cewar Gabkwet.