Shugabannin Binance ɗin sun je Nijeriya ne sakamakon matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na toshe manhajar daga ƙasar a makon jiya, sai dai nan-take ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro ya bayar da umarnin tsare su / Hoto: Reuters

Jami'an tsaron Nijeriya sun tsare biyu daga cikin shugabannin manhajar hada-hadar kuɗin kirifto wato Binance.

Shugabannin Binance ɗin sun je Nijeriya ne bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe manhajar a makon jiya, sai dai ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro ya bayar da umarnin tsare su.

Wata majiya a fadar shugaban Nijeriya ta tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa an tsare shugabannin na Binance ne saboda sun kasa ba da gamsassun bayanai kan yadda manhajar take hada-hadar kuɗi a Nijeriya.

Majiyar, wadda ba ta so a ambaci sunan ta, ta ce manyan batutuwa uku ne suka damu gwamnatin Nijeriya kan hada-hadar ta Binance a ƙasar.

Na ɗaya, kamfanın bai yi rajista da hukumomin ƙasar ba, sannan gwamnati ba ta samun haraji daga ɗimbin ribar da Binance ke samu daga hada-hadar da yake yi a ƙasar, matakin da ke yin illa ga tattalin arzikinta.

Na biyu, babu gamsassun bayanai kan adadin ƴan Nijeriya da ke hulɗa da Binance da kuma yawan kuɗin da ake hada-hadar su.

Na uku, gwamnatin Nijeriya na zargi cewa masu aikata laifukan da suka shafi harkokin kuɗi da masu neman kuɗin fansa suna amfani da manhajar wajen musayar kuɗaɗe ba tare da wata kafa ta iya bibiyarsu don gano abubuwan da suke yi ba.

Kawo yanzu masu manjahar ta Binance ba su ce komai ba game da tsare shugabannin nasu.

Hakan na faruwa ne a yayin da Bayo Onanuga, mai taimaka wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu kan tsare-tsare da watsa labarai, ya ce manhajar ta Binance za ta durƙusar da ƙasar idan ba a kawar da ita ba.

A makon jiya gwamnatin Nijeriya ta zargi Binance da taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin dala a ƙasar da kuma lalacewar darajar naira abin da ya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali.

Wata majiya daga Hukumar Kula da Sadarwa ta Nijeriya NCC ta tabbatarwa TRT Afrika Hausa cewa an bai wa kamfanoni na waya umarnin ɗaukar matakin, kuma har ma an fara aiki da shi, musamman ga masu amfani da waya.

Ranar Talatar da ta wuce, gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya ce wasu mutane da ba su sani ba "sun yi hada-hadar dala biliyan 26 ta manhajar Binance a Nijeriya a cikin shekara ɗaya da ta wuce".

Ya ƙara da cewa hakan yana barazana ga tattalin arziki da tsaron Nijeriya.

TRT Afrika da abokan hulda