Tinubu ya ce batun bai zo gabansa ba ballantana ya amince ko ya yi watsi da shi./Hoto:Fadar shugaban Nijeriya

Fadar shugaban Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa shugaba Bola Tinubu ya amince a kara albashin masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan shari'a a kasar.

Wasu rahotanni sun ambato hukumar tara haraji da kuma kasafta shi ta kasar, RMAFC, tana cewa ta kara albashin shugaban kasa da na mataimakinsa da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kashi 114.

Wannan batu ya ja hankalin 'yan kasar musamman a shafukan sada zumunta inda wasu suka rika sukar gwamnati, suna cewa ta jefa 'yan kasar cikin matsi sakamakon karin farashin fetur amma ita ta kara wa kanta albashi.

Sai dai sanarwar da kakakin shugaban kasar Mr Dele Alake ya fitar ranar Alhamis ta ce "mun bibiyi labarin da aka rika watsawa sosai cewa an kara albashin shugaban kasa da na mataimakinsa da masu rike da mukaman siyasa a gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kashi 114 cike da mamaki.

Muna so mu bayyana karara cewa Shugaba Bola Tinubu bai amince a yi wani karin albashi ba, kuma ba a gabatar masa da wannan batu domin ya yanke hukunci ba."

Sanarwar ta kara da cewa duk da yake shugaban ya fahimci ikon tara haraji da kuma kasafta shi na kayyade haraji da alawus-alawus na masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan shari'a, hakan ba zai tabbata ba sai shugaban kasar ya amince da shi.

Mr Alake ya ce: "Yana da muhimmanci a fahimci cewa RMAFC, ta bakin kakakinta, ta yi raddi kan wannan labari na karya kuma ta fayyace komai.

"Sai dai duk da haka wanna labari da ba shi da tushe ya samu wurin zama a soshiyal midiya da kuma wani bangare na kafafen watsa labarai, abin da ya fito da illar da labaran karya suke da ita ga al'umma," in ji sanarwar.

An kirkiri wannan labari ne a matsayin wani mugun nufi ga gwamnatin Shugaba Tinubu da kuma zummar kashe karsashinsa na ayyukan da yake yi wa 'yan Nijeriya, a cewar kakakin shugaban kasar.

TRT Afrika