Taron kwamitin raba kudi na tarayyar Nijeriya dai ana yi ne tsakanin kwamishinonin kudi na jihohi 36 da kuma ma’aikatar kudi ta tarayya a duka ranar Juma’a ta karshe ta ko wane wata:Hoto/Reuters

Kudin da gwamnatin tarayyar Nijeriya da na jihohi da kuma gwamnatocin kananan hukumomi ke rabarwa wata-wata ya karu da kashi 20 cikin 100 a wannan watan.

Kwamitin raba kudi na tarayyar Nijeriya (FAAC) ya raba naira biliyan 786.2 wanda ya dara naira biliyan 655.9 da ya raba tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kuma gwamnatocin kananan hukumomi a watan da ya gabata.

Wata sanarwar da kwamitin ya fitar ta ce gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 301.889, jihohi suka sami naira biliyan 265.875 yayin da kananan hukumomi suka samu naira biliyan 195.541.

Sanarwar ta ce naira biliyan 786.161 din da aka raba a watan Yuni ya hada da kudin shiga da kudin harajin VAT da harajin tura kudi da sauransu.

Taron kwamitin raba kudi na tarayyar Nijeriya na FAAC din dai ana yi ne tsakanin kwamishinonin kudi na jiha 36 da kuma ma’aikatar kudi ta tarayya a duka ranar Juma’a ta karshe ta ko wane wata.

TRT Afrika