Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada Folashodun Adebisi a matsayin shugaban riko na Babban Bankin kasar, CBN.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin kasar ta ce Mr Adebisi, wanda shi ne mataimakin shugaban Babban Bankin, ya maye gurbin shugaban Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele wanda aka dakatar "nan take".
An dakatar da Mr Emefiele ne bayan an gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.
"An umarci Mr Emefiele da ya yi gaggawar mika harkokin ofishinsa ga Mataimakin Gwamna (Bangaren Gudanarwa), wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Banki na rikon kwarya kafin a kammala bincike da sauye-sauye," in ji sanarwar.
Adebisi shi ne mataimakin shugaban CBN a bangaren gudanarwa tun daga watan Oktoba na 2018.
An haifi Mr. Folashodun Adebisi ranar 7 ga watan Maris na 1962, kuma ya yi digirinsa na farko a fannin Injiniya a Jami'ar Lagos daga 1978 zuwa 1983.
Kazalika ya yi digirinsa na biyu a Jami'ar ta Lagos a fannin Injiniya a 1985. Kana daga bisani ya sake yin diri na biyu a fannin harkokin kudi da kasuwanci daga 1988-1989.
Sabon shugaban CBN ya soma aiki a matsayin injiniya a kamfanin Mek-ind Associates daga 1984 zuwa 1989.
Daga 1989 zuwa 1990, ya zama babban jami'in kasuwanci na kamfanin Inlaks Computers Limited.
A shekarar ta 1990 ya samu aiki a bankin Citibank Nigeria Limited ko da yake ya bar bankin na 1993.
Daga nan Mr Adebisi ya yi aiki a wurare daban-daban da suka hada da Agusto & Co. Ltd da MBC International Limited.
Kazalika ya yi aiki a First City Monument Bank (FCMB) daga 1999 zuwa 2002, da Ecobank Nigeria Plc daga 2003 zuwa 2007 inda ya kama aiki a kamfanin Renaissance Securities Nigeria Limited.
Sabon shugaban rikon na babban bankin Nijeriya ya yi aiki a Union Bank of Nigeria Limited daga watan Satumba na 2009 zuwa Afrilun 2012.
Ya zama manajan daraktan Nigeria Inter-Bank Settlement System Plc daga watan Mayun 2012 zuwa Oktoban 2018.
Daga watan na Oktoban 2018, an nada Mr. Folashodun a matsayin mataimakin shugaban babban bankin Njeriya (bangaren gudanarwa) kuma yana wakiltar shugaban babban bankin a hukumar tattara haraji ta kasar wato FIRS a takaice, tun daga watan Disambar 2019.
Yana da aure da 'ya'ya.