Akalla mutum 2,122 ne suka mutu sannan fiye da 2,421 suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta auka wa kasar Maroko ranar Juma'a, a cewar Ma'aikatar Cikin Gida ta kasar.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ranar Lahadi da maraice ta kara da cewa mutum 1,404 na cikin mawuyacin hali.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.0 ta shafi yankuna da dama da suka hada da El-Houz, Taroudant, Chichaoua, Tiznit, Marrakech, Azilal, Agadir, Casablanca da Youssoufia, a cewar sanarwar.
Girgizar kasar ita ce mafi karfi da kasar da ke Arewacin Afirka ta taba fuskanta a karnin da ya gabata, a cewar Cibiyar Bincike kan Yanayi ta Maroko.
Cibiyar Bincike kan Yanayi ta Amurka (USGS) ta ce girgizar kasar ta faru ne da misali karfe 11 na dare a agogon Maroko, kuma ta kai fadin kilomita 75 (mil 46.6) a yankin da birnin Marrakech mai dimbin tarihi yake, yayin da zurfinta ya kai kilomita 18.5.
Labari mai alaka: Mummunar girgizar kasa ta kashe fiye da mutum 1000 a Morocco
Lamarin ya fi muni a yankin Marrakech inda aka ce gine-gine sun fada kan mutane sun binne su a karkashin kasa.
Kafofin watsa labarai sun ce gine-ginen tarihi, cikinsu har da fitattun ganuwa da ake kira jajayen ganuwa da UNESCO ta ayyana a matsayin wurin tarihi, sun lalace.
Rundunar sojin masarautar kasar ta yi kira ga mutane su yi taka-tsantsan sannan ta nuna musu wuraren da za su matsa domin guje wa kananan motsin kasa.
An ji motsin girgizar kasar a Algeria da Mauritania.
Hukumomin Maroko sun kaddamar da shirin kai tallafi a yankunan da girgizar kasar ta shafa, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar, MAP.
"An tura manyan motocin daukar kaya bakwai dauke da barguna da gadaje da cocilan kauyen Al Arjat da ke birnin Sale na arewaci domin bai wa mutanen da lamarin ya shafa,” in ji MAP.
Kungiyar bayar da agaji ta Turkish Red Crescent ta ce tana bibiyar lamarin sau da kafa kuma tana hada gwiwa da sauran kawayenta na duniya domin kai agaji yankunan da girgizar kasar ta shafa.
Fiye da mutum 600 ne suka mutu sannan da dama suka jikkata yayin wata girgizar kasa mai karfin maki 6.3 da ta auka wa Maroko a 2004.