Karancin kudade da kayan aiki na kawo cikas wurin dakile matsalolin da ke tattare da sauyin yanayi a Afirka. Hoto/Getty Images

A ranar Litinin 4 ga watan Satumba ne za a soma taron Afirka kan sauyin yanayi irinsa na farko a kasar Kenya.

Daga cikin abubuwan da ake sa ran tattaunawa a taron har da batun zuba jari ta bangaren yadda Afirka za ta fuskanci sauyin yanayi da kuma batun yadda za a kara inganta hasashen yanayi.

Ana ganin karancin kayayyakin aiki wadanda za a yi amfani da su wurin samun bayanai kan batun sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da ke ci wa yankin tuwo a kwarya.

Sai dai a halin yanzu, Afirka na da na’urar hasashen yanayi ta radar guda 37, kamar yadda bayanai daga Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya ta bayyana.

Amma Turai kadai tana da na’urar 345 sai kuma yankin Arewacin Amurka na da 291.

Kenya wadda ita ce mai masaukin baki, tana daga cikin kasashe kalilan na Afirka wadda ake ganin tana da na’urarorin hasashen yanayi na zamani, haka Afirka ta Kudu da Morocco.

Kenya ta fitar da kusan dala miliyan 12 a bana domin ayyukan hasashen yanayi, kamar yadda Baitulmalin kasar ya tabbatar.

Idan aka kwatanta da Amurka, kasar ta ware dala biliyan 1.3 a shekarar 2023 domin bangaren na hasashen yanayi.

Haka kuma ita kanta Kenya ta kasashe kasar da ke fama da illolin da ke tattare da sauyin yanayi inda take fama da matslar fari ko kuma karancin ruwan sama tsawon shekaru.

Wannan matsalar ta jawo karancin abinci a kasar da kuma mutuwar dabbobin daji.

Haka kuma a wasu kasashe irin su Nijeriya da Nijar, ana fama da ambaliyar ruwa wadda ita ma ta samo asali ne sakamakon sauyin yanayi.

TRT Afrika