Mazauna wasu yankuna da ake samun ambaliyar ruwa kusan duk shekara a Nijeriya sun shiga fargaba sakamakon sanarwar yiwuwar bude madatsar ruwa ta Lagdo da hukumomin Kamaru suka yi.
Da ma duk shekara sai hukumomin Jamhuriyar Kamaru sun saki ruwan Madatsar Lagdo saboda tumbatsar da take yi, abin da kan janyo mummunar ambaliyar ruwa da ke shafar wasu jihohin Nijeriya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar da sanarwa a ranar 21 ga watan Agusta kan batun, bayan samun sako daga hukumomin Jamhuriyar Kamaru.
Bayan hakan ne hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta fitar da sanarwar cewa hukumomi na daukar matakan hana ta’azzarar lamarin, tare da jan hankalin al’umomin da abin ka iya shafa don daukar matakan da suka dace.
Sai dai ga alama mutanen yankunan da ambaliyar ke shafa duk shekara sakamakon sakin Madatsar Lagdo ba sa daukar wani mataki na guje wa fadawa cikin wannan ibtila’i.
“Babu wani cikakken shiri da muke yi gaskiya, to ina za mu je mu bar dukiyoyinmu," a cewar Malam Muhamman Bapeto, mazaunin kauyen Rugange a Jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da abin ke shafa, a hirarsa da TRT Afrika.
Ya ci gaba da cewa “Illa iyaka dai ba duk shekara ake samun ambaliyar ba, amma gaskiya idan ta faru takan yi muni ta jawo mana asara sosai.”
A ganin Malam Bapeto, ba su ne ya kamata su dauki matakai don guje wa fadawa hadarin ambaliyar ba, “hukumomi ne ya kamata su dinga daukar matakan kare mu da dukiyoyinmu tun da ba wai ruwan damina da ke zuba a yankunanmu ne kawai silar ambaliyar ba."
Sai dai Bapeto, wanda ya ce ambaliyar na dagula musu lissafi sosai, ya ce daga bara suka koyi barin muhallansu su koma wani waje har sai an gama ambaliyar ruwan sannan su koma.
“To, a hakan dai mun samu tsira da rayukanmu da dabbobinmu, amma gidaje da gonaki da kayan amfanin gona haka suke lalacewa gaba daya su bi ruwa, sai dai daga baya idan mun dawo mu sake sabon zubi,” ya fada cikin jajantawa kai.
Labari mai alaka: Za a fuskanci ambaliyar ruwa a Kano, Kaduna, Katsina da jihohi 11 – NEMA
A Jihar Binuwai da ke yankin tsakiyar Nijeriya ma, daya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar bala’in ambaliyar sakin ruwan madatsar ta Kamaru, dubban mutane ne suka shiga fargabar abin da ka je ya zo na barnar da ambliyar za ta yi musu.
Malam Yahaya Jiga-Jigai ya shaida wa TRT Afrika cewa “A yanzu haka mun ga alamar zuwan ruwan, ga ruwan sama yanzu marka-marka da ake yi kullum, mu dai yanzu haka sai addu’a.”
Sai dai duk da cewa a baya ambaliyar ta sha yi musu barna ta dukiya wani lokacin har da rayuka, Malam Yahaya ya ce a bana ma babu wani tanadi da suka yi na daukar mataki illa iyaka suna jiran abin da Allah da hukumomi za su yi.
“Yanzu dai muna ta shawarwari a tsakaninmu mazauna nan yankin, mun dan fara neman mafaka a cikin gari idan har abin ya zo,” a cewar mutumin wanda mazaunin yankin Jibata ne a Jihar Binuwai.
Me ya sa ake sakin ruwan Madatsar Lagdo?
Madatsar Ruwa ta Lagdo na yankin Arewacin Jamhuriyar Kamaru ne kuma an fara gina ta a shekarar 1977 aka kammala a 1982, kuma tana da girman murabba’in kilomita 586.
Madatsar Ruwan na daga nisan kilomita 50 daga birnin Garoua a kan hanyar Kogin Binuwai.
Duk shekara a lokacin damina, ruwan sama kan sa Madatsar Lagdo ta tumbatsa ta yadda har sai an saki ruwan don gudun kada ya jawo wata mummunar barnar.
“Idan har ba a saki ruwan nan ya kwarara ba, to hakika barnar da zai yi za ta ci yankunan Kamaru da yawa ta kuma ci mafi yawan sassan Nijeriya tun daga arewa har yankin kudu maso kudu wato Neja-Delta,” in ji wani masanin Muhalli Dr Ibrahim Mukhtar.
An gina Madatsar Ruwan Lagdo ne don samar da wutar lantarki ga Arewacin Kamaru da kuma ba da damar yin noman rani na kadada 15,000.
Sannan ginin nata ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Nijeriya da Kamaru ne bisa sharadin cewa kowace kasa za ta gina madatsa daya, ta yadda idan na Kamaru ya tumbatsa aka saki ruwan, zai tafi ya shiga Madatsar Ruwan Dasin da Nijeriya za ta gina a Jihar Adamawa don gudun samun ambaliya.
A lokacin yarjejeniyar, an sa ran ita ma Madatsar Dasin za ta samar da megawatt 300 na lantarki tare da ba da damar yin noman rani a fadin hekta 150,000 a jihohin Adamawa da Taraba da Binuwai.
Hukumomi ne ya kamata su dinga daukar matakan kare mu da dukiyoyinmu."
Sai dai tun bayan cimma yarjejeniyar a shekarar 1982, har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta kammala gina Madatsar Dasin ba.
Hakan ya sa idan an saki ruwan Madatsar Lagdo maimakon ya shige Madatsar Dasin da aka yi niyya, sai ya malale ya shige Kogin Benue ya yi ambaliya a jihohin da ke da kogunan da suka hade da na Binuwai din.
“Da gwamnatin Nijeriya za ta yi kokarin kammala aikin Madatsar Dasin a Jihar Adamawa, da hakan zai taimaka gaya wajen rage tasirin barnar da ruwan ke yi,” in ji Dr Ibrahim, wanda kuma malami ne a sashen Ilimin Nazarin Kasa da Muhalli na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
“Don kuwa maimakon ya kwarare ya bi Kogin Binuwai idan an sake shi, to zai ta fi sabuwar madatsar ne, daga nan sai a dinga sakinsa da kadan da kadan,” ya kara da cewa.
Jihohin da sakin ruwan ke shafa
A lokuta da dama sakin ruwan Madatsar Lagdo kan janyo ambaliya da barna mai yawa a jihohin Nijeriya da dama.
A misali a shekarar 2022 kawai, sakin ruwan ya jawo barna mai yawa har da asarar rayuka da lalacewar dumbin gonaki da kadarori na biliyoyin naira a jihohi da dama, inda abin ya fi muni a Jihar Kogi.
A ambaliyar 2022 ta Nijeriya
- Mutum miliyan 1.4 lamarin ya shafa
- Mutum sama da 500 sun mutu
- Gidaje kusan 90,000 ruwa ya shafe
- Jihohi 27 ambaliyar ruwan ta shafa.
A 2019 ma an taba sakin ruwan ba tare da sanarwa ba, inda aka yi mummunar ambaliya a jihohin Adamawa da Taraba da Binuwai da Kogi da yankin Neja-Delta a watannin Okotba da Nuwambar shekarar.
A bana kuwa, hukumomin Nijeriya sun ce sakin ruwan ka iya jawo ambaliya a Adamawa da Taraba da Benue da Nasarawa da Kogi da Filato da Gombe da Bauchi da Anambra da Edo da Delta da kuma Bayelsa.
Hukumomi da al’umma na bukatar daukar matakai
A sanarwar da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta ce hukumomin Kamaru sun sanar musu cewa za su bude kofofin Madatsar Lagdo da ke kan hanyar Kogin Binuwai.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, a cikin sanarwar tata, ta ce tuni ta bai wa shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA umarnin daukar dukkan matakan da suka dace don rage tasirin abin da sakin ruwan ka iya jawowa.
Cikin matakan da ta umarci NEMA ta dauka din har da na wayar da kan al’ummomin da suke rayuwa a yankunan da abin zai shafa don su dauki matakan kariya.
Amma masana irin su Dr Ibrahim na ganin wadannan matakai kawai ba su isa hana tasirin ambaliyar a kan al’ummomi ba.
A ganinsa ya kamata hukumomi su dauki matakai uku masu karfi don magance ibtila’in:
Bincike da tattara bayanai
“Gwamnati na bukatar ta dinga gudanar da cikakken bincike kan yankunan da abin zai shafa, da mutanen da ke zaune a yankunan, da irin girman tasirin da ambaliyar za ta yi a kansu.
“A kuma tattara bayanai a kan dukkan wadannan abubuwa, misali yawan tsofaffi da masu rauni da ke zaune a yankunan, da dukiyoyi da kadarorinsu. Hakan zai ba da dama wajen sanin irin taimakon da za a yi musu tun kafin faruwar abin,” a cewar Dr Ibrahim.
Karfafa NEMA
Masanin na ganin akwai bukatar gwamnati ta kara wa hukumar NEMA karfi na kudade da kayan aiki, ta yadda da zarar bala’in ya faru za ta yi gaggawar amfani da wandancan bayanai na farko da aka tattara ta fara aikin ceton mutane, musmamman marsa karfi sosai.
Kammala gina Madatsar Dasin
Abu na karshe da ya ba da shawarar a yi shi ne a gaggauta kammala gina madatar Dasin da ke karamar hukumar Fufore a Jihar Adamawa, ta yadda idan Kamaru ta saki ruwan Madatsar Lagdo zai gangara ya tafi Dasin.
Sai dai da ma a sanarwar da ta fitar, hukumar NEMA ta ce tana daukar duka wadannan matakan.