Ba kasafai ake ganin afkuwar girgizar kasa a nahiyar Afirka ba / Hoto: Reuters / Hoto: AP

Daga Ebubekir Yahya

A watan Fabrairun da ya gabata ne Turkiyya da makwabciyarta Siriya suka gamu da manyan munanan girgizar kasa da suka yi ajalin sama da mutum 60,000 tare da raba miliyoyi da matsugunansu.

A wasu yankuna da dama an jiyo motsawar kasa sakamakon wannan girgizar da ta afku, musamman ma a yankunan da suke kwance a kan kasa da take gocacciya ko ta kan iya targadewa.

Wasu daga cikin kasashen Afirka na kan irin wannan layi na gocacciyar kasa, wanda ke nuna akwai yiwuwar wata rana a samu girgizar kasa, wanda hakan ke janyo tattaunawa da ce-ce-ku-ce kan hasashen aukuwar ta da ma illar da za a iya samu.

Kasa na shimfide ne a kan wasu faya-fayai na duwatsu da kuma shimfidaddun duwatsun da ko su zama suna bacci ko kuma su zama suna motsawa daga lokaci zuwa lokaci, sakamakon yanayin da suka samu kansu a ciki.

Masana na cewa wadannan duwatsu na manne da juna, idan aka samu gocewar duwatsun ne sai a ce suna da kuskuren daidaituwa.

Wannan gociya na habaka tare da janyo girgizar kasa da a yawancin lokuta take janyo asarar rayuka da dukiyoyi. Girgizar kasa na iya takaituwa ga waje kankani ko yaduwa a yanki mai nisa.

Farfesa Maigari Abubakar malami a sashen nazarin kasa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a Bauchi Nijeriya ya ce “Targadewa ko karyewar faya-fayen kasa na faruwa a yanayi daban-daban duba da yadda suke gugar junansu.”

Kasashen Afirka da ke kan targadaddiyar kasa

A ilimin nazarin motsawa da jujjuyawar kasa an raba yanayin gocewar kasa zuwa kashi uku da suka hada da mai karfi karyayye da matsakaici da kuma juyayye.

Masana sun ce akwai yiwuwar samun girgizar kasa a wasu sassan Afirka wata rana amma hadarin ba mai yawa ba ne /Hoto: Reuters

Bambancinsu shi ne yadda kowanne yake motsawa yake sauka daga kan layi.

Wanda ya fi muni shi ne mai karfi karyayye saboda yadda yake janyo motsawar kasa da karfin gaske wanda hakan ke kawo afkuwar girgizar kasar da ke zuwa da rushewar gine-gine.

Wasu ‘yan kasashe a Tsakiya da Yammaci da Arewacin Afirka na kwance a kan layin gocacciyar kasa inda za a iya samun motsin da zai iya janyo girgizar kasa.

Akwai fargaba a Afirka game da yiwuwar afkuwar girgizar kasa da ake ganin za ta iya yin muni saboda wanzuwar duwatsu da tsaunuka masu aman wuta a wasu yankunan nahiyar.

Wani rahoton hadin gwiwa da UNESCO da Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Afirka da Hukumar Taswirar Kasa ta Duniya suka fitar a 2015 an bayyana wanzuwar gocacciyar kasa a Afirka na saka barazanar yiwuwar samun girgizar kasa babba ko motsawarta.

Ana kallon yankin Yammacin Afirka da ya faro daga Nijeriya zuwa Senagal a matsayin mafi karancin hatsarin fuskantar girgizar kasa, kamar yadda binciken ya bayyana.

A watan Disamban 1983 girgizar kasa mai karfin awo 6.4 ta afku a wannan yankin inda ta fi shafar yankunan kasar Gini tare da kashe kusan mutum 300.

Nazarin ya kuma sake bayyana cewar wani yanki a nahiyar da ke fuskantar barazanar girgizar kasa saboda wanzuwar gocacciyar kasa shi ne Arewa Maso-Yammacin Afirka da ya faro daga Tunisiya zuwa Aljeriya da Murtaniya.

Wata babbar girgizar kasa mai karfin awo 7.2 ta afku a yankin a 1980 tare da janyo asara mai yawa.

Ko nahiyar na kan kasa mai tsaro?

Faya-fayen kasa da suka hade nahiyar waje guda a karkashin kasa suna da targade da gociya.

Yankin da ya fado daga Libiya da Masar ma ya fuskanci girgizar kasa, amma ba ko yaushe ba.

Wannan yanki na kwance a kan gotattun faifan kasa guda biyu – Gociyar Afirka-Yuroshiya da kuma gocaccen faifan tekun Maliya.

Ana kallon yankin Yammacin Afirka da ya faro daga Nijeriya zuwa Senagal a matsayin mafi karancin hatsarin fuskantar girgizar kasa /Hoto: AA

Yankin Afirka na hudu da ka iya fuskantar girgizar kasa shi ne Tsakiyar Afirka, wanda ya hada da gocewar faya-fayen duwatsu masu aman wuta na Kamar da Angola da Chadi da tafkin Kongo.

Na biyar kuma shi ne wani yankin Gabashin Afirka, wanda ya dangana ga Tekun Maliya da Gabar Tekun Aden.

Yanki na karshe da ke fuskantar barazanar girgizar kasa a Afirka shi ne Kudancin Afirka, wanda ya sha samun afkuwar manya da kananan girgizar kasa.

Wannan yanki ya kunshi kasashen Zimbabwe da Mozambique da Bostwana da Zambiya da Angola da Namibiya da Afirka ta Kudu. A 2006 girgizar kasa mai karfin awo 7 ta afku a yankin.

Kamar yadda masanan yanayi da motsawar kasa Farfesa Abubakar ya bayyana, labari mai dadin ji shi ne “Faifan Afirka Kyam yake, wanda ya tattaro daga faifan Tekun Oceanic wanda yake wani bangare na tekunan Atlantika da Indiya.”

Ya yi amanna da cewa babu wata damuwa game da yiwuwar samun babbar girgizar kasa a Afirka irin wadanda aka fuskanta a Turkiyya da Siriya kwanan nan.

Amma kwararru sun yi gargadi kar wannan ya zama dalilin kin daukar matakan kariya don rage radadin barna da illar da girgizar kasa za ta iya janyowa a nahiyar Afirka.

TRT Afrika