Ghana ta yi nasarar rage matsalar yoyon fitsari da kashi 50 cikin 100 a cikin shekara biyar a ƙarƙashin shirinta na kare hana kamuwa da kula da masu lalurar yoyon fitsari (GOFPMSP), kamar yadda hukumar lafiya ta ƙasar ta sanar.
An samar da shirin GOFPMSP na tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021 ne bayan wani kira na tsawon shekara ɗaya da ƙasashen duniya suka yi na yaƙi da yoyon fitsari da kuma ƙoƙarin Ghana na rage yawan cutar zuwaa 2021, da kuma kawar da ita baki ɗaya zuwa 2030.
Sauran muradun shirin sun haɗa da burin kare kamuwa da yoyon fitsari, da inganta tsarin gano masu fama da cutar da kai su asibiti da samar musu da wajen yin jinya da sauran su, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Ghana, GNA ya rawaito.
Farfesa Sebastian Eliason, wanda shi ne jagoran kula da shirin ne ya bayyana wannan nasara a wajen babban taron Kula da Lafiyar Masu ciki da Jarirai da Abinci mai gina jiki na 2023 da wata Hukumar Lafiya ta Ghana ta shirya a Accra.
Taken taron na kwana uku shi ne: “Karfafa tsarin kula da lafiyar mata masu ciki da jarirai don cimma muradu masu ɗorewa.”
Matakan da suka taimaka
Yoyon fitsari wata lalurar lafiya ce da mata ke haɗuwa da ita yawanci a wajen haihuwa, inda al’aurarsu ke haɗewa da wajen ba-haya.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai mata daga tsakanin 50,000 zuwa 100,000 da ke fama da cutar a fadin duniya a duk shekara.
Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Ghana da UNFPA suka fitar a 2015, ta ƙiyasta cewa duk shekara ana samun sabbin masu matsalar yoyon fitsari 1.6 zuwa 1.8 a duk haihuwa 1,000 da ake yi.
Dr Eliason ya ce an samu nasarorin rage cutar ne saboda inganta fannin kula da lafiyar mata da tabbatar da samun kulawa a lokacin renon ciki da ƙara yawan ungozomomi a cibiyoyin lafiya da kuma sanya matsalar yoyon fitsatri a cikin tsarin Inshorar Lafiya, da sauran su.
Ya bayyana cewa a shekarar 2017 lokacin da aka samar da shirin, yawan masu fama da yoyon fitsari ya ragu daga 540 zuwa 206 a 2021.
Sai dai ya ce duk da tarin nasarar da aka samu har yanzu akwai masu fama da lalurar sosai saboda rashin isasshen tsarin kai wa wasu yankunan da masu yoyon fitsarin suke, da rashin ingantaccen tsarin samar da kudade da kuma rashin isassun abokan hulɗa da sauran su.
Ya yi kira kan a ƙirƙiri tsarin wayar da kai a kan ilimin yoyon fitsari da wani shiri na bai wa masu lalurar da likitocin gundumomi horo kan yadda za su dinga kula da masu lalurar.