Matuƙin jirgi yana zauna a kan jirgin yaƙin Faransa yayin da Faransa ta fara janye sojojinta daga Chadi. / Hoto: Reuters

Ma'aikatar Tsaron Chadi ta ce Faransa ta fara janye sojojinta daga Chadi a ranar Juma'a, bayan N'Djamena ta kawo karshen hadin gwiwar soji da tsohuwar wacce ta yi mata mulkin mallaka a watan da ya gabata.

Tawagar sojoji 120 ta tashi zuwa Faransa daga filin jirgin saman soji da ke babban birnin Chadi, kwanaki 10 bayan wani jirgin yakin Faransa ya bar ƙasar ta yankin Sahel, kamar yadda wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a shafin Facebook.

Ƙasar Chadi dai ta kasance wata babbar gada da ta haɗa Faransa da nahiyar Afirka, kuma waje na karshe da ta ajiye sojojinta a yankin Sahel, bayan ficewar sojojin Faransa daga Mali da Burkina Faso da Nijar, bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasashen.

Amma a ranar 28 ga Nuwamba Chadi ta ba da sanarwar kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro da Paris, wacce aka fara tun daga samun 'yancin kai a 1960.

'Sun kama hanyar Faransa'

"Da tsakar rana, sojojin Faransa 120 sun tashi daga filin jirgin saman soja na N'Djamena a wani jirgin Airbus A330 Phoenix MRTT, wanda ya nufi Faransa," in ji ma'aikatar a cikin sanarwar ta Facebook.

Rundunar sojan Faransa wacce ke da dakaru kusan 1,000 a Chadi ba ta ce uffan ba kan sanarwar.

Sanarwar ta ce, tashin sojojin na Faransa a ranar Juma'a ta faru ne a gaban hukumomin sojin na Chadi, matakin da ke tabbatar da tsananin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin tsaro.

Sojojin Faransa da jiragen yakin Faransa sun kasance a kasar Chadi kusan tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, inda suke taimaka wa wajen horar da sojojin Chadi.

Yanke alakar soji

Matakin da Chadi ta ɗauka na yanke hulɗar soji da Faransa ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya kai, abin da ya nuna cewa tawagarsa ba ta da masaniya kan matakin.

Ƙasar da ke Tsakiyar Afirka ita ce ƙasa ta ƙarshe a yankin Sahel da ta karɓi baƙuncin sojojin Faransa.

Har ila yau, matakin na ta ya zo ne jim kaɗan bayan da Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, ya kamata Faransa ta rufe sansanonin sojinta da ke ƙasar ta Yammacin Afirka.

Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Chadi ta fitar ta ce, kayan aikin soja za su bar kasar a cikin jirgin Antonov 124 da aka shirya yi a kwanaki masu zuwa.

Har ila yau sanarwar ta ƙara da cewa, ana shirin mayar da motocin soji daga sansanonin Faransa guda uku zuwa Faransa ta tashar ruwan Douala ta Kamaru.

A baya dai shugaban na Chadi ya taɓa cewa, kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro ba ta nufin "watsi da hadin gwiwar kasa da kasa, ko kuma sanya alamar tambaya kan alakar diflomasiyyarmu da Faransa ko ta wane hali".

TRT Afrika