Mutanen da suka rasa muhallansu suna tattara kayayyakinsu a lokacin da suke barin sansanin 'yan gudun hijira na Bulengo. / Hoto: AFP

'Yan tawayen M23 waɗanda ke samun goyon bayan Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo sun rufe wasu sansanin gudun hijira karfi da yaji, lamarin da ya ja fiye da mutum 110,000 suka rasa muhallansu a 'yan kwanakin nan, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya da mazauna yankin suka tabbatar.

Kungiyar M23 ta ba da wa'adin sa'o'i 72 ga mutanen da suka rasa matsugunansu da su bar sansanonin gudun hijira, su koma garuruwansu, in ji hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, a cikin jawabinta a ranar Talata.

Wannan dai shi ne mataki na baya-bayan nan da 'yan tawayen suka ɗauka bayan da suka ce abin da suka sa a gaba shi ne a koma gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba a baya.

Ko da yake daga baya 'yan tawayen sun fayyace cewa mutum sai yana so zai koma bisa raɗin kansa, OCHA ta fiye da mutane 110,000 da suka rasa matsugunansu ne suka bar irin wadannan sansanonin zuwa kauyuka masu nisa da kungiyoyin agaji suka yi gargadin cewa suna da nisa daga kai agaji.

"Na yi mamaki saboda an ce mu tafi, amma duk da haka ba ni da wani abin da zan ba yara," in ji Sibomana Safari, wanda ke barin sansanin 'yan gudun hijira na Bulengo a birnin. "Dukkanmu (za mu tafi) ba tare da wani taimako ba (kuma) ban sani ba ko za mu yi hakan," in ji Safari.

Akalla mutane 500,000 ne suka rasa matsugunansu a yankin sakamakon yadda kungiyar ta M23 take ƙara mamaye wurare, a cewar gamayyar kungiyoyin sa-kai na kasa da kasa suka tabbatar.

Goma dai ta karbi bakuncin mutane kusan miliyan guda da suka rasa matsugunansu kafin barkewar fada a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kwimana Sifa, wanda ke cikin wadanda suka bar sansanin gudun hijira na Bulengo, ya ce ba shi da wurin zuwa bayan wani bam ya lalata gidansa.

"Ya fi kyautuwa a bar mu a nan. Ko da yake ba mu da abinci, amma muna da matsuguni a nan," in ji Sifa a cikin damuwa. "Abin da muke so shi ne zaman lafiya ba wani abu ba."

TRT World
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince