Akwai Boda-Boda miliyan uku da suke da rajista a Uganda. Hoto/Reuters

Daga Kudra Maliro

Sama da shekara 30 bayan da aka fara amfani da babura domin yin acaba a garin Busia da ke kan iyakar Uganda, Boda-Boda ya zama wani nau’in sufuri wanda da wuya yake bayar da kunya – ta fannin samunsa da saukin kudinsa da kuma saurinsa.

Ko da mutum ya samu kansa a cikin cunkoso ko kuma yana neman hanyar fita wajen gari, babura sun fi sauki ta wannan fannin.

'Asalin boda-boda'

Boda-Boda ya samo asali ne daga “border-border”, wato iyaka-iyaka, inda a farko ake amfani da babur din domin safarar kayayyaki daga Uganda zuwa Kenya.

Tun a lokacin da aka fara amfani da su a Busia a 1988, wadannan baburan sun bazu zuwa garuruwa da dama a Uganda, a hankali kuma zuwa Gabashi da Tsakiya da Yammacin Afirka.

Ana amfani da Boda-Boda a kauyuka da birane. Hoto/Reuters

"Labarin yadda aka samar da Boda-Boda daga keke zuwa babur abu ne mai jan hankali. Zuwa 1982, Uganda na samar da rake mai dumbin yawa wanda ake bukatar a rinka fitar da shi.

Tun da dai yana da wahala ga manoma su rinka fitar da kayayyakin gonarsu zuwa Kenya da keke, sai ‘yan kasuwa da dama suka yanke shawarar shigo da babura daga Asia domin magance matsalolin sufuri.

Abin da aka soma amfani da shi domin magance matsalar jigilar gahawa da rake daga Busia zuwa Kenya sai ya yi sauri ya zama wani kasuwanci na jifar tsuntsu biyu da dutse daya.

“Wadannan masu baburan suna zuwa Kenya da kaya sai a hanyarsu ta dawowa su dauko mutane. Don haka sunan ‘border-to-border, sai ya koma Boda-Boda daga baya,” in ji Vincent Kisiriko, wanda dan jarida ne na kasar Uganda da ke Kampala kuma marubucin wani littafi kan batun fadada Boda-Boda a Gabashin Afirka, ya shaida wa TRT Afrika.

Tun daga shekarun 1980, babura sun kasance hanyoyin da ake kaunar amfani da su domin sufuri a Gabashin Afirka. Hoto/Reuters

A lokacin, akwai tsada siyan wadannan babura, duk da dai ana cewa ba su da shan mai sosai.

Kisiriko ya tuna da cewa kusan shekarar 2000, Uganda ta fuskanci habaka a bangaren sufuri inda aka shigar da MATE, wani nau’in babur wanda ake kera shi a Japan.

Domin samun saukin sufuri ga matafiya, sai Boda-Boda ya kara suna sosai.

A yau, a Gabashin Afirka da sauran sassan yankin, matafiya wadanda cunkoson ababen hawa ke takuramawa sun fi son samun sauki ta hanyar hawa Boda-Boda a maimakon tasi ko bas-bas.

Girma da habaka

Boda-Boda na matukar taimaka wa dubban mutane domin samun ayyuka. Hoto/Reuters

Kamar yadda wani rahoto da aka wallafa a Maris din 2023 da hukumar gudanarwa ta Kampala, akwai sama da Boda-Boda masu rajista 150,000 a birnin na Uganda kadai, inda kuma aka yi kiyasin akwai miliyan uku a Gabashi da Tsakiyar Afirka.

Domin tsallaka iyakar Uganda zuwa Kenya, matukin Boda-Boda na bukatar na bukatar lasisin tuki wanda kudinsa ya kai dala 180 da kuma biyan dala 20 a matsayin kudin yada zango.

‘Boda-Boda a tafin hannu’

Matafiya a kasashen Gabashin Afirka a halin yanzu za su iya amfani da waya domin kiran Boda-Boda daga ko ina. Uganda ta soma amfani da wasu irin fasahohi domin kula da habakar bangaren duk da masu sana’o’i na komawa zuwa amfani da fasahar zamani domin samun riba.

Safeboda wata manhaja ce wadda take bayar da dama ga fasinjoji su yi odar babur din, inda baburan suke dauke da hular kwano inda matukan ake horas da su dokokin hanya.

Ana amfani da manhaja domin kiran Boda-Boda. Hoto/Reuters

Wani rahoto da aka wallafa a 2013 wanda Standard Bank ya yi ya nuna cewa Boda-Boda zai iya zama bangare mafi girma da zai rinka samar da kudin shiga a Uganda baya ga noma.

A Kenya, bangaren a halin yanzu yana samar da dala miliyan hudu a rana, kamar yadda kungiyar masu babura ta Kenya ta bayyana.

A Tanzania, akwai dubban matasa da ke shiga sana’ar Boda- Boda a duk shekara, duk da cewa batun yanayin tsaronsu wani abin damuwa ne. Kamar yadda kididdigar gwamnati ta nuna, Tanzania ta shigo da babura 1,884 a 2003.

A bara, babura 185,110 aka shigar da su kasar, wadanda akasarinsu domin yin haya da su. “Boda-Boda na taimakawa matuka ga tattalin arzikin Uganda. Ka yi tunanin cewa akwai wadannan miliyoyin baburan da ke yawo ko ina a fadin kasar a kullum,” in ji Kisiriko.

Sharif Nsubuga, wani mahaifi mai shekara 30, ya kasance mai tuka Boda-Boda tsawon shekara shida a Kampala.

Yana tashi a kullum da misalin hudu na safe domin fita a cikin birnin, inda yake daukar mutane daga gidajensu zuwa wuraren aikinsu. Yana aiki matuka inda a rana bai komawa gida sai wurin goma na dare.

Kiyayewa na da muhimmanci matuka ga matuka babura da kwastamominsu. Hoto/Reuters

“Ina samun kusan dala 15 a duk rana a matsayina na mai tuka Boda-Boda bayan na kashe kudi kan akalla lita uku ta mai akalla a rana,” in ji Nsubuga. Matashin yana tara kudi domin sayen babur cikin biyu ko uku domin ya ci gaba da karatunsa, wanda ya daina shekara shida da suka gabata.

Ya bayyana cewa aikinsa akwai hatsari kuma akwai rikici sakamakon cunkoson ababen hawan Kampala, amma ya saba da haka.

A Gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyya Kongo, an fara amfani da Boda-Boda a farkon shekarun 2000, a lokacin da da ‘yan kasuwar Kongo ke tafiya zuwa Uganda da Kenya inda suka ga baburan suka soma amfani da su domin tafiye-tafiye.

Kambale Manoke, wani dan kasuwa daga Beni, yana daga cikin wadanda suka soma amfani da Boda-Boda a Gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo. Batun ya soma zuwa masa a 1998 bayan da ya tafi zuwa Kampala ya sayi kaya. “Wani abokina dan Uganda ya taho da ni domin ya yi siyayya.

Domin yin zagaye, sai ya ce na hau Boda-Boda. Sai na yi tunani kan cewa idan na sayi babur a nan Uganda domin amfani da shi a Beni, zan yi irin haka domin na samu kudi,” in ji shi.

Hoto/Reuters

Manoke ya tuna da yadda tuka babur a Beni yake wani abu na kasaita. “Mutane da dama suna biyan kudi domin su hau babur ba tare da sun san inda za su ba.

A birane uku masu girma na gabashin Jamhuriyyar Kongo, a halin yanzu muna da Boda-Boda sama da miliyan daya,” in ji shi.

TRT Afrika