Yan takara fiye da goma ne suka fafata a zaɓen shugaban ƙasar. / Hoto GNA

Ɗan takarar shugaban ƙasar Ghana Mahamudu Bawumia na jam’iyya mai mulki ta NPP ya amince da shan kaye a hannun tsohon shugaban ƙasar John Dramani Mahama na Jam’iyyar NDC a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

Mista Bawumia ya amince da shan kayen ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Lahadi inda ya ce bisa alƙaluman da suka fito dangane da zaɓen a halin yanzu, alamu sun nuna Mista Mahama ne ya lashe zaɓen ƙasar.

“Bayan zaɓen da aka gudanar na shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa a jiya, ‘yan Ghana da ke cikin gida da ƙasashen waje suna ta jiran tsammani domin jin sakamakon zaɓen,” kamar yadda Bawumia ya bayyana.

“Dangane da alƙaluman da muka tattara daga ɓangarenmu na zaɓe alami sun nuna tsohon shugaban ƙasa John Dramani Mahama ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

“Haka kuma NDC ɗin ta lashe zaɓen ‘yan majalisa duk da cewa muna jiran sakamakon zaɓe na ƙarshe da za a tattara na wasu kujeru,” kamar yadda Bawumia ya ƙara da cewa.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar Jam’iyyar NDC John Mahama ya sanar da cewa Bawumia ya kirasa a waya inda ya taya sa murnar lashe zaɓen ƙasar. Mista Mahama ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X a ranar Lahadi

Yan takara fiye da goma ne suka fafata a zaɓen shugaban ƙasar, sai dai 'yan takara biyu ne dama can ake ganin tsakaninsu ne wani zai lashe zaɓen, wato Mahamudu Bawumia, na jam'iyyar New Patriotic Party, mai mulkin ƙasar, da kuma tsohon shugaban ƙasa John Dramani Mahama na jam'iyyar National Democratic Congress (NDC).

TRT Afrika