Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya halarci taron Kasashen Gabashin Afirka IGAD karo na 42 a Entebbe/ Hoto: Reuters

Somalia ta ce ba za ta yi sulhu da Ethiopia ba sai birnin Addis Ababa ya soke yarjejeniya mai cike da ce-ce-ku-ce ta yin amfani da tashar jiragen ruwa da ya kulla da yankin Somaliland da ya balle daga kasar.

"Ba za mu bude wata kofa ta sulhu da Habasha ba sai ta janye daga haramtacciyar yarjejeniyar sannan ta amince da 'yancin Somalia na kasancewa kasa mai gashin kanta," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Somalia a wani sako da ta wallafa a soshiyal midiya ranar Alhamis.

Kasashen biyu sun dade suna rigima kan batun iyakoki, inda suka yi yaki sau biyu a karshen karni na 20.

Ranar Alhamis gwamnatin Somaliland ta yi zargin cewa da gangan Somalia "ta karya alkawuran da ta yi a baya da Somaliland" ciki har da batun tsaro da amfani da sararin samaniya.

Ta yi zargin ne bayan Hukumar Kula Da Sararin Samaniyar Somalia ta ce ta hana jirgin saman Ethiopian Airlines sauka a Hargeisa, babbar birnin Somaliland ranar Laraba.

Kazalika ranar Alhamis, hukumar ta hana wani jirgin daukar kaya da aka yi wa rajista a Thailand shiga sararin samaniyar Somalia domin isa Hargeisa daga birnin Sharjah na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kwamitin Sulhu na Kungiyar Tarayyar Afirka ranar Laraba ta yi kira ga makwabtan biyu su "yi taka-tsantsan, su daina tayar da jijiyoyin wuya sanna su yi tattaunawar da za ta wanzar da zaman lafiya".

TRT Afrika da abokan hulda